Yadda jakunkunan audugar mata ke taimaka wa ƴanmata zuwa makaranta

Yadda jakunkunan audugar mata ke taimaka wa ƴanmata zuwa makaranta

Wata mai ƙaramar sana'a a Uganda ta samar da wata jakka wadda ba ta jiƙewa koda a cikin ruwa, wadda ke ke tatso hasken rana kuma an haɗa ta ne daga abubuwan da aka sake sarrafawa - domin taimaka wa ƴanmata su riƙa zuwa makaranta.

Kowace jakka na ƙunshe da fitila mai amfani da hasken rana, da audugar mata wadda ake iya amfani da ita fiye da sau ɗaya, da littafi kan tsaftace jiki a lokacin jinin al'ada da kuma kayan ɗinki.

Fitilar na taimaka wa yara wajen karatu hatta a wuraren da babu lantarki. Sai kuma audugar mata da littafin faɗakarwa kan tsafta a lokacin jinin al'ada domin taimaka wa yara mata wajen yin tsafta.

Ya zuwa yanzu an raba irin waɗannan jakkuna guda 12,000, inda ake sa ran raba irin su guda miliyan ɗaya a faɗin gabashin nahiyar Afirka.