Kotu ta ce Muhammad Abacha ne dan takarar gwamnan Kano a PDP

Abacha

Asalin hoton, Facebook/Muhammed Abacha

Babbar Kotun Tarayya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke hukuncin cewa Muhammad Abacha ne ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

Mai Shari'a AM Liman ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis ta manhajar Zoom kasancewar baya gari.

Ya ce bangaren da suka gudanar da zaben fitar da gwani a Lugard Road shi ne halastaccen zaben dan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP, kasancewar jami’an hukumar INEC sun halarci wurin tare da sanya ido kan zaben.

Tun bayan ficewar Rabi'u Musa Kwankwaso ne rikici ya ƙara ƙamari a jam'iyyar PDP ta Kano ta yadda har aka samu rarrabuwar kawuna a zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar gwamna.

Ɓangaren Aminu Wali ya fitar da ɗan takararsa Sadiq Wali yayin da ɓangaren Shehu Sagagi ya fitar da Muhammad Abacha a matsayin nasa ɗan takarar.

A zaben fitar da gwani da aka yi a watan Mayun 2022 Mohammed Abacha ya fafata da Adamu Yunusa Ɗan Gwani da Ibrahim Al-Amin Little da Muhiyi Magaji Rimin Gado da Jafar Sani Bello da kuma Injiniya Mu'azu Magaji wato Ɗan Sarauniya.

Kuma a lokacin sakamakon ya nuna Muhammad din ne ya yi nasara.

Sai dai a watan Yuli kuma sai ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta wallafa sunan Sadiq Aminu-Wali a matsayin dan takarar PDP na jihar Kano.

Me Muhammad Abacha ya ce?

Barista Sa’idu Muhammad Tudun Wada shi ne lauyan Muhammad Abacha ya yi wa BBC arin bayani kan hukuncin kotun.

"A cikin hukuncin da kotun ta yi, ta yi umarni a kan cewa INEC ta cire sunan Sadiq Wali ta musanya shi da sunan Muhammad Abacha bisa hujjojin da ta dogara da su cewa shi ne sahihin dan takara wanda jam'iyya ta gabatar kuma INEC ta halatta."

Ya ce alkalin ya ƙara da cewa "rashin bayar da sanarwa ta kwana 21 kamar yadda dokar zaɓe ta tanada, ita jam'iyyar PDP a matakin ƙasa da ta gaza yi na bai wa INEC sanarwa, wannan ya jawo tasgaro a kan sahihancin zaɓen da aka yi a filin wasa na Sani Abacha."

'Ba mu yarda ba'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai lauyan Sadiq Wali wanda yanzu sunansa ke gaban hukumar zabe a matsayin dan takarar gwamna a PDP, ya ce ba su gamsu da hukuncin ba, amma za su tattauna da wanda yake karewar don daukar mataki na gaba.

Farfesa Nasiru Adamu Aliyu ya ƙara da cewa "alkali bai yi la'akari da cewa akwai hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano ta yanke a sati biyun da suka wuce, a kan zaɓe makamancin wannan ba.

"Dama abin guda biyu ne, ta ce duk zaɓe da jam'iyya ta yi, ta ja ba ta da hurumi, zaɓenta ba shi da tasiri, sannan wanda ya yi ƙarar ma ba shi da ikon kai wa ƙara.

"Bisa wannan abin da za mu yi shi ne zan saurari wanda nake wakilta na ji ra'ayinsa, amma zan ba shi shawara cewa akwai hujja mai ƙwari daga hukuncinsa da na ji.

"Ina ganin kamar akwai hujja 15 da ke nuna hukuncin kuskure ne.

"Domin bai kamata a yi hukunci saɓanin wanda kotunan sama suka yi ba, wato Kotun Ƙoli da Kotun Ɗaukaka Ƙara, wadanda suka ce duk zaɓen da ɓangaren jiha ya yi, to ba shi da tasiri kuma ba shi da amfani," a cewar Farfesa Nasiru.