Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum mai mata 12 da yara 102
Mutum mai mata 12 da yara 102
Mazaunin wani ƙauye a Uganda, mai suna Musa Hashaya Kasera ya ce iyalansa sun ƙunshi da yara 102, da jikoki 578.
Musa mai shekara 68 a duniya ya ce "na fuskanci matsaloli wajen sanya yarana makaranta, da ciyarwa da tufatar da su, da kuma kiwon lafiyarsu."