"Tun ina da shekara 12 na kamu da HIV"
"Tun ina da shekara 12 na kamu da HIV"
Binta, wata matashiya ce da ta kamu da cuta mai karya karguwar da ake kira HIV, wadda ta kiyaye shan magani har ta kai matakin da ba a iya ganin ƙwayar cutar a jininta yanzu.
Matashyar, wadda ta ce yanzu sun fi so ana kiran su da AYP wato Adolescents and Young People, ta ce tana fafutika ne domin wayar da kan masu ɗauke da cutar domin su fahimci rayuwa, kuma su gan cewa suma mutane ne kamar kowa.
Ta ce matuƙar mai cutar na shan magani, za su kai matakin da take yanzu, na wanda ba za a cutar a jikinsu ba, kuma ba za su yaɗa ba.



