Ɓeran da ke kintsa tarkace a rumfar wani mutum cikin dare
- Marubuci, Daga Charlie Buckland
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Duk da kasancewarsa mai tsananin sha'awar ɗaukar hotunan namun daji, kuma tsohon ma'aikacin aika saƙonni, Rodney Holbrook bai taɓa tsammanin zai ɗauki bidiyon wani abin al'ajabi da ke faruwa a rumfarsa ba.
Bayan a karo da dama ya gano cewa cikin dare wani abu mai kama da mu'ujiza na faruwa, inda yakan wayi gari ya ga duk an kawar da tarkacen da ya zubar, sai ya kafa kyamara a kan teburin aikinsa.
Ta dai ɗauki bidiyon wani ɓera da ke tsittsince tarkace kamar noti da ƙusoshi da maɗaurai da maƙata.
Dattijon mai shekara 75 daga yankin Builth Wells, cikin ƙasar Wales, ya ce tsawon wata biyu kenan da ya fara lura da halayyar kakkauda tarkacen da ake yi a rumfar tasa.
"Da farko na lura cewa idan na zuba wa tsuntsaye abinci, sai a kwashe a zuba a cikin wasu tsofaffin takalma da na ajiye a cikin rumfar," in ji shi.

Asalin hoton, ANIMAL NEWS AGENCY
"A mafi yawan lokuta ɓeran zai kwashe tsawon dare yana tsittsince tarkace, ya kawar a wuri ɗaya.
"Abin ya wuce hankali ganin cewa yana zuba duk abubuwan da ya tsince ne a cikin wani ɗan akwati, ina kyautata zaton mai yiwuwa yana jin daɗin aikin da yake yi."
Mista Holbrook ya yi imani ɓeran na amfani da akwatin ne don ɓoye notuna, kuma zuwa yanzu kaude-kauden da yake yi, yana yi wa mai rumfar daidai.
"Ba na damuwa na ɗaɗɗauke tarkace don kawar da su gefe ɗaya yanzu, nakan bar komai yashe a wajen akwati, shi kuma kafin safiya, sai ya kwashe ya mayar inda ya dace," in ji shi.
"Kai ina jin, wata rana ko matata na bari, zai janye ta, ya kai ya adana."

Asalin hoton, ANIMAL NEWS AGENCY
Kusan babu wani ɗan ƙaramin tarkace wanda ga alama yake gagarar ɓeran, don kuwa an gan shi yana kawar da wayar ɗaukan tukunya.
"A gaskiya ma dai, na yi ta jarraba shi, inda nake ƙara abubuwa iri daban-daban a kan teburin don na ga ko zai iya ɗauka," a cewar Mista Holbrook.
Ba karon farko ba kenan da dattijon yake gamuwa da ɓerayen da ke gyara wuri.
Lokacin da yake zaune a Bristol cikin shekara ta 2019, abokinsa ya taɓa neman taimakon ya je ya gyara masa kyamarar ɗaukan bidiyon dare, bayan ya lura da wani ɓera da ke kikkintsa tarkace a rumfarsu.
"Hoton bidiyon wancan ɓeran shi ma ya karaɗe gari kuma ya yi tashe sosai, mutane sun kalle shi a faɗin duniya," ya ce,
"To na kasa yarda cewa a nan ma Builth Wells, mun samu irin wannan ɓera bayan shekaru da wancan da na sani."



