Tashin farashin Gas ɗin girki na ƙara damun magidanta a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Rabiatu Kabir Runka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News hausa
Ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa game da yadda farashin gas ɗin girki ya yi tashin gwauron-zabi a baya-bayan nan.
A wasu wurare a jihar Kano ana sayar da kilo ɗaya na gas din kan naira 1,000 wasu kuma 1,100.
Wannan na zuwa ne yayin da bayanai ke cewa abubuwa da dama ne suka haddasa tsadar gas din ciki har da karancinsa.
Bayanan da BBC ta samu na cewa farashin gas din na ci gaba da tashi a sassan Najeriya.
Tukunyar gas ɗin girki mai nauyin kilo 12 a yanzu ana sayar da ita a kan 12,000, a wasu wuraren kuma fiye da haka.
Wani mai sayen gas a Kano, Sanusi Mannir Garba ya shaida wa BBC cewa" yanzu na zo sayen kilo 12 kuma na saye shi a kan 10,900, saɓanin a baya da muke saye kan 8900."
"Muna amfani da gas din a jikin Janareto a shagonmu na ɗinki saboda tsadar fetur, idan muka sayi kilo12 yana kai mana kwana biyu da wuni saboda injin da muke amfani da shi babba ne," in ji Sanusi Mannir.
Abdullahi Muhammad ya shaida wa BBC cewa gas ɗin ba ya jimawa yake ƙarewa, lamarin da ya tursasa musu haɗawa da gawayi wajen yin girki.
"Mun samu an ƙara masa kuɗi, tunda a baya ana sayar da kilo kan 750 amma yanzu ga shi ya doshi 900 har 1,000 ma, ina da kilo biyar amma kilo uku na iya saye saboda tsada."
Me ya haddasa tsadar gas ɗin ?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Basiru Sulaiman Iliyasu wani mai sayar da gas din a Kano, ya ce suna shan wahala kafin su samu gas ɗin daga wurin manyan diloli.
"Abin da yake faruwa yanzu shi ne ana shan wahala kafin a samu gas ɗin, sannan farashin ya ƙaru ga kuma kudin ɗaukowa, idan muka je kamfani da kyar muke iya samun guda ko biyu a hakan ma kafin a samu ana shan wahala, sai dai addu'a kawai," In ji Basiru Sulaiman.
"Muna sayar da kilo guda na gas din kan naira 1,000, muna cika kilo 12 kan naira dubu 12,000, wasu wuraren suna sayarwa kan naira 1,100 ko 1,050, sakamakon wahalar da ake sha kafin a same shi da kuma tsadar kudin kai wa, wasu daga wajen gari suke shiga gari su sawo," In ji Sulaiman.
Wani babban dillalin man fetur a Arewacin Najeriya, Bashir Ahmad ɗan Malam ya shaida wa BBC cewa "rashin kyawun hanya ne ke ƙara ta'azzara lamarin."
Rahotanni na cewa akwai fargabar farashin zai iya ƙara tashi saboda karancin gas din, kasancewar ba ya samuwa sosai.
Wannan yanayi da ake ciki dai, mai yiwuwa zai sake haifar da matsi musamman tsakanin masu karamin karfi da ke kukan tsadar rayuwa a kullum, tun bayan janye tallafin man fetur da ake zargin ya haddasa hauhawar farashi.










