'Ba dukkan kuraje da ke fitowa yara ba ne cutar kurga'

Bayanan bidiyo, 'Ba dukkan kuraje da ke fitowa yara ba ne cutar kurga'
'Ba dukkan kuraje da ke fitowa yara ba ne cutar kurga'

Danna hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Tun a ranar litinin 11 ga watan Yuni ne muka fara kawo muku jerin bidiyo kan lafiyar yara da muka yiwa lakabi da camfe-camfe kan yara kanana.

Wannan bidiyon shi ne na karshe, kuma ya dubi yadda wasu iyaye da yawa suke barin 'ya'yansu ba tare da nema musu magani ba idan kuraje suka fitowa yaran.

Akasari iyayen yara su na cewa cutar kurga ce ke damun 'ya'yan nasu ba tare da la'akari da bincike na kiwon lafiya ba.

Likitocin yara kamar su Dakta Naja'atu Hamza ta ce "a wasu lokuta akwai wasu kuraje da ke saka fatar yara ta yi haske ko kuma ta yi ja, kuma kurajen ba na kurga ba ne".

Ta kara da cewa a wasu lokuta cutar suga ce ke kawo irin wadannan kuraje idan aka bincika.

"Idan yaro yana da ciwon suga yakan samu yawan kuraje a matse-matsinsa".

Al'umma da dama a sassa daban-daban na nahiyar Afirka sun yarda da wasu camfe-camfe a kan yara kanana da kuma sauran abubuwa da suka shafi rayuwarsu.

Akasarin wadannan camfe-camfen ba su da tushe a kimiyyance.