Larabawa, 'yan Afirka ko ƙabilar Amazigh? Ce-ce-ku-ce a kan asalin 'yan Moroko

Asalin hoton, Reuters
A jerin wasikun da muke samu daga 'yan jaridarmu na Afirka, Magdi Abdelhadi ya duba mana yadda kwallon kafa ta janyo rikici kan ko su wane ne mutanen Moroko.
______________________
Ba a yi karin gishiri ba idan aka ce Gasar Kofin Duniya ta ƙwallon ƙafa da aka yi a kasar Qatar a bana ta janyo ce-ce-ku-ce sama da na baya.
Kama daga bai wa Qatar damar karbar bakuncin gasar, duk da zarge-zargen keta hakkin bil'adama da ake yi wa kasar, zuwa karshen gasar lokacin da sarkin kasar ya sanya wa gwarzon dan wasa kuma dan kasar Argentina, Lionel Messi alkyabba, gabannin ya daga kofin cin gasar a ranar Lahadi.
Sai dai akwai wata takaddamar da bata ja hankali sosai ba a wajen yankin da kasar ta ke wato arewacin Afrika.
Tambayar da ta janyo wannan cece-kucen ita ce ta yadda za a bayyana kungiyar kwallon kafa ta Morocco.
Za a kira su ne da sunansu na Atlas Lions, kungiyar da ta bai wa duniya mamaki, saboda irin gagarumar ruwan da ta taka.
Kamar murkushe kungiyoyin da ake ji da su na kasashen Spaniya da Portugal.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shin za a kira 'yan kungiyar kwallon kafa ta Morocco da ta Larabawa ta farko ko ta Afrika ta farko da ta kai zagayen na kusa da na karshe?
A al'adance mafiya yawan al'ummar kasar na daukar kansu a matsayin Larabawa fiye da ce musu 'yan Afrika.
Sannan wasu 'yan kasashen kudu da hamadar Sahara da ke zaune a kasar na korafin cewa, nuna bambancin launin fata ba wani abu ne boyayye ba a kasar.
Amma tsokacin da dan wasan gaba na gefe, Sofiane Boufal, ya yi bayan kasarsa ta doke Spaniya, ya janyo muhawara kan ko a wace nahiya kasar take.
Ya mika godiya ga "dukkanin 'yan Morocco a fadin duniya saboda goyon bayan da suka bayar, kuma ga dukkanin Larabawa da Musulmi baki daya. Wannan nasara taku ce gaba daya."
Amma ya sha matukar suka ne a kafafen sada zumunta, ya je shafin Instagram yana bayar da hakuri kan rashin ambaton goyon bayan da 'yan Afrika suka bai wa kungiyar.
Kamar yadda Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce Moroko ta "fid da mara ɗa kunya ta janyo abin alfahari ga nahiyar da irin gwanintar da suka yi."

Asalin hoton, AFP
Chastened, Boufal ya wallafa cewa: " Na kuma na mika wannan nasara a gare ku. Muna alfaharin wakiltar dukkanin 'yan uwa da ke nahiyar, Muna tare " Matukar murnar da aka nuna na da alaka da yunkurin da masarautar kasar ta yi na baya-bayan nan na yaukaka dangantaka da sauran nahiyar Afrika.
"Afrika gidana ne kuma zan komo gida," Sarki Mohammed VI ya fadi hakan a shekarar 2017 a yayin da aka sake karbar Morocco a cikin kungiyar tarayyar Afrika, bayan shafe shekara 30 da ficewarta kan batun yakin Saharawi da ake takaddama a kansa.
Wannan alaƙar ta sa harkokin kasuwanci sun haɓaka, musamman ma da ƙasashen Afirka ta Yamma.
Amma Moroko mamba ce a ƙungiyar Tarayyar Larabawa ta Arab League. Saboda haka ƙasar na da alaƙa da ɓangarorin biyu. Yayin amfani da kalmar "Afirka" wajen siffanta Moroko ke nufin yankin da suka fito, amfani da kalmar "Larabawa" a kansu na jawo ɓacin rai daga waɗanda ba sa so a siffanta su da hakan.
Akwai 'yan ƙabilar Berber masu yawa a Moroko, kom kuma Amazigh kamar yadda suke kiran kansu - an yi ƙiyasin za su kai kashi 40 cikin 100 na ɗaukacin al'ummar ƙasar kusan miliyan 34.
Yanzu haka an saka harshen Tamazight - babba daga cikin harsunan Amazigh - cikin harsuna na hukuma a Moroko bayan Larabci.
Sai dai kuma wannan rikici ne da ya daɗe yana faruwa ƙasa-ƙasa. Jim kaɗan bayan an bai wa Qatar damar ɗaukar nauyin Gsar Kofin Duniya, ƙasar ta bayyana hakan a matsayin "nasara ga Musulunci da Larabawa", kamar yadda rahotanni suka bayyana a 2010.
Yayin da aka fara gasar kuma, kalmomin Musulunci da Larabci sai suka shige ba a harkokin.
Yayin da ake rikici kan hana shan giya da haramcin saka tsimman kyaftin mai goyon bayan 'yan luwaɗi da aka kira OneLove, masu goyon bayan Musulunci da harkokin Larabawa sun kare Qatar da kuma addinin daga abin da suka kira hari daga "ƙasashen Yamma 'yan mulkin mallaka".

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai abin da kafofin yaɗa labarai na Qatar suka dinga kwatanta gasar da shi cewa "nasarar Musulunci da Larabawa", wanda ba a lura da shi ba sosai, ya jawo martani cikin fushi lokacin da aka fara saka al'amuran a cikin sharhin wasannin gasar.
Saboda haka, lokacin da tawagar Atlas Lions ta Moroko ta zama ƙsar Afirka da Larabawa ta farko da ta kai wasan kusa da ƙarshe a gasar, an yi ta kwatanta hakan da nasarar Musulunci da ƙasashen Larabawa.
Bayan an fitar da ƙasashen Larabawa - Saudiyya da Tunisya da Qatar - daga gasar, da ma an yi tsammanin magoya baya ba su da wani zaɓi illa su goya wa Moroko baya.
Sai dai wasu ƙungiyoyi sun so su bayyana nasarar ta Moroko a matsayin abu muhimmi fiye da haka, wanda ya fi alaƙa da siyasa ko aƙida.
Daga baya sai aka mayar da Moroko wakiliyar Musulunci da Larabawa.
Wannan batu ya sake ƙarfafa bayan wasu 'yan wasan Moroko sun buɗe tutar Falasɗinu a cikin fili don yin murna.
Irin wannan yunƙuri ya ɓata wa mutane da yawa rai a Arewacin Afirka, musamman 'yan Moroko da ba sa alaƙnta kansu da irin waɗannan aƙidun da kuma yadda ake kallon su a duniya.
'Cin karo tsakanin al'adu'
Cikin wani bidiyo da ya shafe awa kusan ɗaya yana magana, wani ɗan Moroko ma'abocin dandalin YouTube ya caccaki mutanen da suka yi ƙoƙarin siyasantar da gasar tare da mayar da ita kamar yaƙi tsakanin al'adu.
Mutumin mai suna Brother Rachid ya tuna wa masu bin shafinsa 385,000 cewa rabin 'yan wasan tawagar Moroko an haife su kuma sun taso a Turai, waɗanda akasarinsu 'ya'yan 'yan ci-rani ne 'yan Moroko da suka taso suka koyi buga ƙwallon a Turai.
"Da za a yi wa tawagar gwajin ƙwayar halitta na DNA, za a ga cewa akasarinsu Amazigh ne. Da yawansu ba sa jin Larabci, idan ma suna ji to sai dai Larabcin buroka saboda a Turai suka taso," kamar yadda ya ce.

Asalin hoton, Getty Images
Sauran masu suka sun nuna damuwa game da yadda aka mayar da ƙwallon ƙafa abin addini ko kuma na al'adu, suna masu cewa ba abin da zai yiwu ba ne a ce idan Brazil ko Argentina suka yi nasara a ce nasara ce ga Kiristanci.
Sun faɗi haka ne saboda ganin irin cakuɗuwar da ke tsakanin al'ummomin ƙasashen, musamman na Turai.
Wannan taƙddama game da ainahin ƙabilar 'yan wasan Moroko ita ce ta baya-bayan nan da ke nuna "adawa tsakanin ƙabilu" a Arewacin Afirka wadda ta daɗe tana ruruwa.











