Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
...Daga Bakin Mai Ita tare da maman Maryam ta Labarina
...Daga Bakin Mai Ita tare da maman Maryam ta Labarina
Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan mako ya karɓi baƙuncin Rahama Sidi Ali, wadda aka fi sani da maman Maryam a cikin fim ɗin Labarina.
Rahama haifaffiyar garin Kaduna ce amma iyayenta 'yan asalin ƙasar Ghana ne.
Ta yi fina-finai kamar Kwana Casa'in, da Farar Mace kafin ta shahara sosai a fim ɗin Labarina mai dogon zango na kamfanin Saira Movies.