Yadda Tinubu ke facaka na nuna bai damu da talaka ba - Dino Melaye

Yadda Tinubu ke facaka na nuna bai damu da talaka ba - Dino Melaye

Wani babban ɗan'adawa daga jam'iyyar haɗaka ta ADC ya ce har yanzu 'yan Nijeriya suna mutuwa sanadin yunwa da matsin rayuwa, waɗanda manufofin Tinubu suka jefa su.

Sanata Dino Melaye ya yi iƙirarin cewa Shugaba Tinubu bai cika ko ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗaukar wa al'umma ba.

Tsohon ɗan majalisar dattijan ya zargi shugaban Nijeriya da kashe-kashen kuɗi na facaka ta hanyar sayen jirgin ruwan alfarma da danƙareren jirgin sama da kuma motar da babu irinta.