Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wumdiyo: Garin da ya zama wajibi a sanya keken hawa cikin kayan lefe
Wumdiyo: Garin da ya zama wajibi a sanya keken hawa cikin kayan lefe
Keke na ɗaya daga cikin hanyoyin sufuri da suka yi suna a duniya, sai dai a Najeriya an yi watsi da shi kasancewar ana yi masa kallon raini a cikin al'umma.
Sai dai keke abu ne mai matuƙar muhimmanci a tsakanin al'ummar Margi da ke jihar Borno a arewacin Najeriya ta yadda ake buƙatarshi a cikin kayan lefe na aure.
Bidiyo: Ayuba Iliya @ay_iliya
Tacewa: Abba Auwalu