'Yadda cutar sikila ta sa na shafe shekara takwas a karatun difloma'
'Yadda cutar sikila ta sa na shafe shekara takwas a karatun difloma'
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
To duk da ci gaban da aka samu a fagen magance jinyar da masu lalurar sikila ke yi, musamman a bangaren dashen da ake yi musu na bargon kashi wanda ke iya warkar da su sarai, har yanzu mawuyacin halin da wasunsu ke ciki sai kara ta'azzara yake yi.
Cikin irin wadannan masu jinyar akwai wata matashiya mazauniyar birnin Zariya, wadda lamarinta ya kasance mai sosa rai, amma ta kasance wadda ta jajirce a fagen neman ilimi, har a bana ta kai ga zama mai yi wa kasa hidima bayan ta shafe shekaru takwas tana kokarin kammala karatun babbar difloma.
Abokin aikinmu Sani Aliyu ya ziyarci wannan matashiyar a gidansu, ga kuma yadda hirarsu da ita ta kasance.



