Ko Majalisa za ta iya kawo ƙarshen sayar da takardun aiki a Najeriya?

Majalisar Wakilai tana zuba ido don karɓar rahoto a farkon watan gobe daga wani kwamiti da ta ɗora wa alhakin bankaɗo duk wata badaƙala da ake zargi wajen ɗaukar ma'aikata da almundahanar sayar da takardun aiki a Najeriya.
Badaƙalar ɗaukar sabbin ma'aikata da sayar da takardun aiki, wata babbar annoba ce da ake zargin ta dabaibaye ma'aikatu da hukumomin ƙasar, a matakan gwamnatin tarayya da na jihohi.
Akwai zargi daga ɓangarori masu yawa na haɗa baki da manyan jami'an gwamnati wajen wofintar da cancanta da gogewa har ma da ƙwarewa, inda ake sayar da guraben aiki ga mutumin da ya fi biyan kuɗi masu tsoka.
Da yake gabatar da ƙudurin da ya kai ga kafa kwamitin binciken a ranar Laraba, wani ɗan majalisa, Oluwole Oke mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Oriade/ Obokun, ya ce yanzu cin hanci da rashawa sun mamaye harkar ɗaukar ma'aikata a Najeriya.
Ya kuma yi iƙirarin cewa hatta manyan makarantun Najeriya, sun daina tallata ɗaukar sabbin ma'aikata.
Ya ce ko 'yan ƙalilan da ake tallatawa, kawai ana yi ne, amma a zahiri tuni sun rigaya sun sayar da guraben aikin, a kan maƙudan kuɗi.
Ɗan majalisar ya zargi ma'aikatu da hukumomin gwamnati da tafka almundahana wajen gudanar da Dunƙulallen Tsarin Tattara Bayanai da Biyan Ma'aikata mai taken IPPIS a taƙaice, ta hanyar ɓullo da dabarun cusa ma'aikatan bogi.
Majalisar wakilan dai ta ce tana sane da ƙoƙarin da gwamnati ke yi, na magance matsalolin da ke addabar tsarin, ciki har da ƙoƙarin kakkaɓe ma'aikatan bogi.
Masharhanta da dama a Najeriya ga dukkan alamu, ba su da ƙwarin gwiwa a kan wannan bincike, mai yiwuwa bisa la'akari da girman wannan matsala da yadda kusan ta zama ruwan dare a ƙasar.
Duk da yake, ɓangarori da yawa za su so zuba ido su ga hanzari da gudun ruwan majalisar, game da ko ma da gaske za ta iya gudanar da wani zuzzurfan bincike daidai girman matsalar a cikin wata ɗaya. Shin tana iya bankaɗo manyan jami'an gwamnatin da ake zargi suna cin gajiyar wannan badaƙala?
Yaya sakamakon binciken da kwamitin zai gabatar a cikin watan Agusta, zai kasance? Ko za a ɗauki matakan hukunci da ɓullo da tsare-tsare masu inganci don kawar irin waɗannan badaƙaloli?
Duka waɗannan tambayoyi ne da 'yan Najeriya masu yawa za su so sanin amsoshinsu.

Asalin hoton, Getty Images
'An nemi na biya naira miliyan uku don a ba ni aiki'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kusan dai a iya cewa al'adar da aka san matasan da suka kammala karatu ke yi a shekarun baya, ta zuwa ƙafa-da-ƙafa kamfanoni da ofisoshin hukumomin gwamnati da ma'aikatu, ta zama tsohon yayi.
Tasirin neman aiki ta hanyar da ake yi wa laƙabi da "Wa-Ka-Sani, Wa-Ya-San-Ka", ita ma tana raguwa.
Yanzu, ko ka san wani, sai ka tanadi dubban ɗaruruwan nairorin da za ka biya, kafin ka karɓi ofa. Sai dai fa, idan wanin nan da ka sani, lallai ya kai, ya kawo a cikin gwamnati.
Su kansu, 'yan majalisar dokokin da za su yi wannan bincike, suna cikin igiyar zargi, don kuwa a yanzu, ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ake auna ƙwazon ɗan majalisa a Najeriya, har da adadin matasan mazaɓarsa da ya samar wa aiki a ma'aikatu da hukumomi.
Mai yiwuwa ne, wasu 'yan majalisar, dalilin kyakkyawar alaƙar da suke da ita da wasu jami'an ɓangaren zartarwa, suna iya samun wata alfarma, amma dai yawan rahotannin da ake ji "na rabon offer" daga 'yan majalisar, abu ne da ke ƙarfafa zargin yadda ake kashe-mu-raba da sayar da takardun aiki daga hukumomi da ma'aikatu.
Akwai ma manyan hukumomi ko kamfanonin gwamnati waɗanda kusan kwata-kwata ba a sanin lokacin da suke ɗaukar ma'aikata.
Wasu dai na zargin cewa irin waɗannan wuraren aiki masu matuƙar maiƙo, ana keɓe su ne kawai yanzu ga 'ya'ya da makusantan manyan jami'an gwamnati da 'yan siyasa, sai kuma waɗanda rabonsu ya rantse.
Badaƙalar sayar da guraben aiki, babbar matsala ce da ta daɗe tana ci wa 'yan ƙasar tuwo a ƙwarya, musamman matasan da suka zage damtse wajen neman ilmi a manyan makarantu da jami'o'i, cike da fatan samun wata hanyar halaliya bisa cancanta ta aikin yi, don hidimtawa ƙasa da kuma gina rayuwarsu ta ƙashin kai.
Matsala ce mai sanyaya gwiwar al'ummar ƙasa musamman masu ƙaramin ƙarfi da dakushe kyakkyawar ɗabi'ar aiki tuƙuru da wofintar ƙoƙarin neman halaliya.
Wani matashi da ya taɓa neman aiki a wata babbar ma'aikatar gwamnatin tarayya ya shaida wa BBC game da yadda aka buƙaci ya biya miliyoyin naira kafin a ba shi takardar aiki.
Matashin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya yi zargin cewa wasu manyan jami'an ma'aikatu ne ke raba guraben aiki a tsakaninsu, inda wasunsu ke sayar da guraben ga masu tsananin buƙata.
"Shekara shida da ta wuce, an haɗa ni da wani babban mutum da ya kai darakta, a kan cewa zai samar min aiki, amma da na hadu da shi sai ya ce sai na biya naira miliyan uku tukunna", in ji matashin.
Ya ci gaba da cewa saboda ba shi da wannan kuɗi dole yana ji yana gani wannan aiki ya wuce shi, bai samu ba.
'Matsalar ta zama ruwan dare'
A baya-bayan nan, hukumar yaƙi da almundahanar kuɗi ta ICPC ta bayyana gurfanar da wani mataimakin darakta a ofishin babban akanta na ƙasa, bisa zargin aikata zamba wajen ɗaukar ma'aikata.
Cikin wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ranar Laraba, ICPC ta ce ta kai mataimakin daraktan gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ne, tare da wani jami'i a hukumar bunƙasa binciken sararin samaniya ta ƙasa (NASRDA) bisa zargin damfara da zamba wajen ɗaukar aiki da kuma haɗa baki.
ICPC ta gabatar da tuhuma shida a kan mutanen biyu da ta ƙunshi haɗa baki da tozarta muƙami da damfarar wasu masu neman aiki kuɗi har kusan naira miliyan uku.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
A watan Janairun 2022 ma, babbar kotun jihar Bauci ta samu wani mutum mai suna Ibrahim Abubakar da laifin damfarar wani mai neman aiki kimanin naira miliyan biyu da dubu ɗari biyu da hamsin da sunan zai samar masa aiki a hukumar TETFUND.
Jaridar Premium Times ta ambato hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC na cewa alƙalin kotun ya ɗaure Ibrahim Abubakar shekara uku a gidan yari da zaɓin biyan tara, bayan an karɓo kuɗin da ya damfari mai neman aikin.
Ko a ranar 20 ga watan Maris ɗin 2023, hukumar EFCC cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce wani alƙali a Kaduna Mai shari'a A.A Bello ya samu wani Ahmad Kabiru Gana da laifin zambar ɗaukar aiki bayan ya karɓi naira 287,000 bisa alƙawarin samar wa wani matashi aikin ɗan sanda, amma ya gaza yin hakan a tsakanin watan Satumba zuwa Oktoban 2021.
Kotun dai ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara biyar a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira 100,000.
A baya-bayan nan ma ranar 4 ga watan Afrilun 2023, babbar kotun jihar Kano ƙarƙashin Mai shari'a Hadiza Suleiman, ta samu wani mutum mai suna Ahmad Sultan Sardauna da laifi, kuma ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara huɗu a gidan yari.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da mutumin a kotu tare da wani mai suna Emmanuel Tunde bisa tuhumar haɗa baki da yin jabun takardu da nufin damfarar wani ɗan ƙasar Somaliya $4,661 da sunan za su samar masa aiki da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Haka zalika, a cikin watan Nuwamban 2022, hukumar ICPC ta yi nasara a kotu, inda alƙali ya samu wani jami'in hukumar tsaron farar hula ta (NSCDC) da laifi, bayan an tuhume shi da damfarar wata 'yar Najeriya N100,000, don ya taimaka wajen samar mata aiki a hukumar.
Babbar kotun jihar Osun dai ta yanke wa jami'in mai muƙamin sufurtanda a hukumar ta sibil defensi, Segun Odewale hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari.
Mun tuntuɓi daraktan wayar da kai da ilmantarwa a ICPC, Muhammad Ashiru Baba don jin ko me suke gani da wannan bincike na majalisar wakilan Najeriya, dangane da wannan matsala?
Jami'in dai ya ce ICPC na maraba da wannan yunƙuri.
A cewarsa, hukumar ta kama mutane masu yawa bisa zargin aikata badaƙalar ɗaukar aiki ko sayar da gurbin aiki, tare da gurfanar da su a kotu.
"Abin da ya kamata hukumomi su yi shi ne, su bi abin da doka ta ce game da ɗaukar ma'aikata, ta yadda za a tallata aiki, sannan mutane su nema, kuma a kira su a gana da su don sanin ko sun cika ƙa'ida kuma sun cancanta, ta yadda za a ɗauki waɗanda suka dace," in ji daraktan.
Sai dai a karo da dama, ba haka ce take faruwa ba a Najeriya.
Ya ce daɗa ƙazancewa da matsalar ta yi, ya tilasta wa hukumar ICPC ƙara ɓullo da matakan yaƙi da wannan badaƙala.
A ciki har da ƙwace kuɗin da aka biyan don sayen wani gurbin aiki. "Yanzu duk mutumin da ya bayar da kuɗi don a ba shi aiki, to idan bincike ya biyo ta kansa ba za a mayar masa da kuɗin ba," a cewar Muhammad Baba.
"Mun yi gangamin wayar da kai, don sanar da 'yan Najeriya cewa su daina sayen aiki. Saboda haka daga yanzu muna gargaɗi duk wanda aka kawo masa aiki ya saya, ko mun kama wanda ya sayar masa da gurbin aikin, to shi wanda aka zaluntar ba za mu mayar masa da kuɗin ba''.
Gurgunta aikin gwamnati
Daraktan wayar da kan na hukumar ICP ya ce matsalar sayen gurbin aiki, na da babbar illa ga harkar aikin gwamnati don kuwa zai kashe ƙwazon aiki kuma zai ƙarfafa gwiwar cin hanci da rashawa a ƙasar.
"Domin duk wanda ya sa kuɗi ya sayi aiki, to tunaninsa shi ne yadda zai mayar da kudin ya kashe sannan ya samu riba, to don haka ba zai mayar da hankali wajen yin aikin da aka ɗauke shi ya yi ba", in ji Ashiru Baba.
A cewar ɗan majalisar wakilai, Oluwole Oke badaƙala a tsarin ɗaukar aiki, na haifar da asarar biliyoyin kuɗi duk wata wajen biyan albashi ga ɗumbin ma'aikatan bogi a matakan gwamnati daban-daban.
Matakin da ka iya zama wani babban kalubale da zai iya gurgunta tsarin aikin gwamnati a Najeriya.
Ya ce ''idan aka duba tarihi, daga 1960 zuwa 1990, tsarin aikin gwamnatin Najeriya, na cikin mafiya inganci a duniya, wanda ke gudana bisa ƙwarewa".
"To amma sannu a hankali wannan inganci ya riƙa zaizayewa, saboda hanyoyin da ake amfani da su yanzu wajen ɗaukar ma'aikata a hukumomin gwamnati, waɗanda ke tattare da zamba da cin hanci da kuma wasu abubuwan da ba na ƙa'ida ba ne''.











