Laifuka bakwai da ka iya sanya ma'aikatan gwamnati a Najeriya su rasa aikinsu

Bayanan bidiyo, Laifuka bakwai da ka iya sanya ma'aikatan Najeriya rasa aikinsu

Ku latsa alamar wannan hoto na sama domin kallon hira da farfesa

Wata matsala da ma’aikatan gwamnati da masu rike da ofisoshin gwamnatin ke fuskanta a Najeriya ita ce hukuncin da ke biyo baya sakamakon rashin bayyana kadarorinsu ga hukumar Da’ar Ma’aikata.

Bisa tsarin aikin gwamnati dai ya kamata duk wani ma’aikaci ya bayyana kadarar tasa ta yadda da an gan shi yana kashe abin da wuce kima za a iya bincikarsa.

Farfesa Muhammad Awwal, shugaban hukumar Da’ar Ma’aikata ta Najeriya ya shaida BBC cewa a yanzu haka sun mika takardun gurfanarwa na ma’aikata fiye da dari shida a gaban kotun Da’ar ta Ma’aikata bisa rashin bayyana kadara ko kuma rashin Da’a.

Farfesa Muhammad Awwal ya lissafa wasu laifuka guda bakwai da ya ce "za su iya sa wa a kori ma'aikacin gwamnati kuma a haramta masa aikin har na tsawon shekara goma ciki har da kin bayyana kadara"