'Yadda ciwon suga ya sauya min rayuwa'
'Yadda ciwon suga ya sauya min rayuwa'
Alhaji Zubairu Tanko Sulaiman ya kamu da ciwon suga a 2002, amma sai a 2015 ciwon ya yi tsananin da har sai da aka yanke ƙafarsa ta hagu.
Ya faɗa wa BBC cewa ciwon ya sauya rayuwarsa ƙwarai da gaske, saboda a yanzu ba shi iya fita neman kuɗi kuma ba zai iya yin bara ba.
Mazaunin jihar Nasarawa a arewacin Najeriya, Zubairu ya bayyana tashin farashin magungunan cutar a matsayin babban abin da ya fi damunsa.



