''Yata ta sha suma saboda cin zali da ta yi fama da shi a makaranta'
Damuwar da al'ummar duniya ke nunawa tana karuwa, a kan bukatar tsare lafiyar kwakwalwar dalibai masu koyon ilmi da koshin lafiyarsu, in ji Asusun kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (Unicef).
Asusun ya ce manufar makarantu, su kasance muhalli mai aminci da tallafawa masu koyon ilmi da malamai, sai dai shaida ta nuna ba haka ne ke samuwa ba.
Ga mutane da dama, makarantu sun zama wuraren da ake nuna tashin hankali da cin zalin da ke iya addabar kowa.
Wannan wani bangare ne na wayar da kai game da Ranar Yaki da Cin Zali ta Duniya, wadda ake tunawa da ita duk rana irin-ta-yau, 2 ga watan Nuwamba.
Gangamin na kokarin nuna kwakkwarar alakar da ke akwai tsakanin nuna tashin hankali a makaranta da kuma lafiyar kwakwalwa.
Taken ranar ta bana dai, shi ne "Ba za a lamunci bayar da tsoro ba: Kawo karshen tasar wa mutum hankali a makaranta don inganta lafiyar kwakwalwa da koyon ilmi".
Cikin nau'o'in cin zalin da ake kokawa da su har da na sabuwar hanyar rayuwa wato intanet, da manufar kawo ƙarshen tashin hankali a makarantu don inganta lafiyar ƙwaƙwalwar yara da koyon iliminsu.
BBC ta samu zantawa da wata uwa wadda ta ce irin wannan cin zarafi ya yi sanadin mutuwar 'yarta bayan kwashe shekaru suna jinyar tsananin damuwar da ta shiga.
Mahaifiyar mai suna Hauwa Ahmad Aminu da ke jihar Kano, ta ce a dalilin haka ne ma, ta kafa gidauniya domin wayar da kai game da cin zalin yara a makarantu.
'Kusan duk wanda ya yi makaranta ya taɓa fama da matsalar'
"Ba duka ake magana ba, idan aka ce cin zali a makaranta, ko kuma idan aka ce cin zarafi, a zaci ta hanyar lalata.
"Magana ake ta faɗawa yaro ko yarinya magana da za ta yi ta ci masa rai, ta tsaya masa a zuciya, ta janyo masa koma baya wajen fahimta da saurin koyo.
"A mafi yawan lokuta kalmomin ne na muzantawa, ta hanyar tanka siffofin halittar jiki ko 'yan gidansu ko kuma ƙoƙarinsu a makaranta," in ji Hauwa Ahmad.
A cewarta, idan abubuwan suka ta'azzara yara suna shiga matsananciyar damuwa, kuma hakan kan shafi kwakwalwarsu.

Asalin hoton, YOBE STATE GOVERNMENT
A cewar wannan mahaifiya matsalar cin zali ko cin zarafi a makarantu babba ce, domin kuwa ta zama wata ɗabi'a tsakanin ɗalibai.
"Duk wanda ya yi makaranta ya san tsananin tasirin wannan matsala, abin da ya sa ba a nuna damuwa sosai a kai shi ne, ƙarancin tasirin matsalar tsakanin yara a baya.
"Amma a yanzu wannan abu na tasiri kuma har ya haifar musu da koma baya a ɓangaren koyo," in ji Hauwa.
Irin waɗannan kalaman muzantawa na fitowa daga bakin malaman yaran a wasu lokutan, a matsayin hukunci idan sun yi musu laifi, in ji ta.
Malami kan iya kallon yaro su ce masa "mai kunnuwa kamar fanke" shi kenan daga nan sai ɗalibai 'yan uwansa su ɗauka.
Dole sai suma malamai sun kiyaye irin wannan kalaman da illar da suke yi.
'Shekaru muka yi muna jinyarta, ta mutu daga ƙarshe'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hauwa ta ce lokacin 'yarta na aji ukun farko na sakandire sai aka yi mata shugabar dalibai, abin da ya haifar da kishi tsakaninta da wata abokiyar karantunta.
Wannan yasa ita abokiyar tata ta gama kai da wasu kawayenta irin 'marasa jin nan' wannan ya sa suka riƙa yi mata barazana da rayuwarta.
Hakan ya haifar mata da tsoro kuma ya sa ta shiga tsananin damuwa, har ta zo ta fara jijjiga.
"Shekara bakwai muka kwashe muna zuwa asibiti, duk inda muka je sai a ce damuwa ta riga ta yi mata illa a kwakwalwarta. Daga nan kwakwalwar ta fara shanyewa har ta yi sanadiyyar rayuwarta".
Mahaifiyar ta ce ba su kai ga gano wannan matsala da ruwi ba balle su sauya wa 'yar tasu makaranta ko kuma su kai koke ga hukumomi.
Sai da aka kwashe shekara biyu tana haɗiyar wannan damuwa da baƙin ciki, ba ta faɗa ba balle a san halin da take ciki saboda tsoro.
"Randa abin ya bayyana suma ta yi, sai da ta yi kwana biyar a sume, ba a san me ya sameta ba.
"Da ta farka likita ya ce mata Zainab barka da farfaɗowa, sai ta cewa likitan ba ta son ta mutu, sai ya ce wanene ya ce za ki mutu?, sai ta sake suma," in ji mahaifiyar.
A cewar mahaifiyar ta shiga damuwa kafin mutuwarta yawanci abin yakan fara mata da matsanancin ciwon kai, sai ka ji ta kwalla kara shi kenan.
"A matsayina na uwa ko me zan faɗa mutane ba za su gane raɗaɗin da na ke ji ba na tsawon wannan shekaru tun bayan mutuwarta.
Ta bai wa iyaye shawarar riƙa jan yaransu a jiki ta yadda za su sake da su, su riƙa shaida masu damuwarsu kan abin ya ta'azzara.
Ta ce da an ga yaro baya shiga cikin 'yan uwansa yara kamar wanda ake tsangwama, to a yi maza a ji meke damun shi.
Iyaye su kasance masu nazarin halayyar 'ya'yansu ta yadda da sun sauya za su iya maza su fahimta.












