Binciken da ya janyo dakatar da 'digiri ɗan Kwatano' a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Zukatan ‘yan Najeriya da dama sun cika da karsashi, kuma ana ta mayar da martani ga matakin da hukumomi suka ɗauka a kan shaidar karatun digirin da ake yi wa laƙabi da digiri ‘yar Kwatano a ƙasar.
Matakin ya zo ne kwanaki ƙalilan bayan wani binciken ƙwaƙaf da wani ɗan jarida ya yi ta hanyar samun shaidar karatun digiri cikin ƙasa da wata biyu, har ma ya shiga aikin hidimar ƙasa da takardar digirin da ya samu daga birnin Kwatano na ƙasar Benin.
Binciken da wakilin jaridar Daily Nigerian ta intanet ya yi ya bankaɗo yadda ake iya sayen "ilmin digiri" daga jami'ar ƙasar Benin, har ma ya jawo gwamnatin Najeriya ta dakatar da karɓar shaidar karatun jami'o'in Benin ɗin da kuma Togo.
Da ma an daɗe ana zargin jami''o'in Benin da bayar da shaidar digiri cikin watanni ƙalilan maimakon shakara huɗu da aka saba yin sa.
Sai dai lamarin ya ƙara ƙamari ne a baya-bayan nan, inda wasu ke samun shaidar digirin cikin sauƙi kuma a 'yan makonni, kuma wannan shi ne dalilin da ya sa jaridar ta ɗauki gabarar gudanar da binciken.
"A da idan mutum ya faɗi jarrabawa a jami'a a Najeriya ya zama abin tausayi, amma yanzu kuna tsaka da tausaya masa sai ku ga shi har ya shiga sansanin hidimar ƙasa na NYSC," in ji Jaafar Jaafar shugaba kuma babban editan jaridar Daily Nigerian.
Jaafar ya ce sun kwashe kusan shekara ɗaya suna gudanar da binciken tare da tallafi daga wasu cibiyoyi da ke tallafa wa ayyukan jarida a ciki da wajen Najeriya.
Yadda ɗan jarida ya yi 'digirin shekara huɗu' cikin mako shida
A watan Disamban 2022, wakilin na Daily Nigerian mai suna Umar Audu ya fara tuntuɓar wani mutum wanda eja ne da ya ƙware wajen sayar da takardun digiri daga ƙasashe maƙwabta a kan farashi "mai sauƙi".
Mutumin ya ba shi zaɓin "yin karatu" na shekara ɗaya ko kuma watanni, shi kuma ya zaɓi watanni.
"Ba matsala ba ce, za mu iya taiamaka maka indai akwai kuɗi," in ji mutumin. "Mun yi wa wasu da yawa, idan ka biya kuɗin yanzu za a iya samun shaidar a wata mai zuwa."
Mutumin ya nemi a biya kuɗin karatu, da na takardar tantancewa, da na shaidar zama a Benin, da na bugun hatimin hukumar shida da fice a kan iyakar Benin da Najeriya.
Kamar da ƙasa, ɗan jaridar ya samu takardun shaidar kammala digiri a fannin sadarwa ko kuma aikin jarida daga jami'ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies, ESGT, Cotonou, Benin Republic a ranar 17 ga watan Fabarairun 2023.

Asalin hoton, Daily Nigerian
Takardun sakamakon da aka ba shi sun nuna cewa ɗan jaridar ya fara karatu a makarantar da ke da alaƙa da wata jami'a a 2018 kuma ya kammala ranar 5 ga watan Satumban 2022.
'NYSC sun yi ƙoƙari amma har yanzu akwai matsala'

Asalin hoton, Daily Nigerian
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bisa doka, duk ɗalibin da ya kammala karatun digiri ko babbar difiloma ta ƙasa, wajibi ne ya je bautar ƙasa matuƙar bai wuce shekara 30 da haihuwa ba a lokacin gamawarsa.
Duk shekara dubban ɗalibai ne hukumar ke tantancewa don tura su sansanonin hukumar ta National Youth Service Corp a faɗin ƙasar, ciki har da waɗanda suka yi karatu a ƙasashen waje kamar Benin da Togo.
Haramcin da gwamnatin Najeriyar ta sanar na nufin an dakatar da dukkan ɗaliban da suka samu shaidar digiri daga Benin ko Togo shiga hidimar ƙasar.
A takardun shaidar da aka fara aika wa ɗan jaridar, an yi kuskuren bayyana jinsinsa a matsayin mace, abin da ya sa ya nemi a mayar da shi Kwatano don a gayara.
"Saboda ba mu so a samu matsala nan gaba ko kuma wajen tura shi hidimar ƙasa, shi ya sa muka ce sai an gyara," a cewar Jaafar. "Muka biya kuɗin mota aka je aka kawo sabon sakamako wanda ya nuna cewa namiji ne shi."
Sai dai ɗan jaridar ya fuskanci matsala lokacin da ya miƙa shaidar zama a Benin (residence permit) don tantancewa a NYSC, inda suka ce ta jabu ce kuma suka kore shi.
"Suka ce sai ya kawo fasfo ɗinsa da ke nuna cewa ya shiga ƙasar kuma ya fita. Da ma ya yi fasfo ɗin saboda wannan aiki, kuma ya samu wani eja ɗin daga hukumar shiga da fice ta Najeriya da ya karɓi fasfo kuma suka buga masa cewa ya shiga ya fita.
"An buga hatimi na shiga da fitarsa kusan sau 10 duk da cewa bai taɓa zuwa iyakar Najeriya da Benin ba balle ma ya fita. Daga nan ne kuma NYSC suka ƙyale shi ya je hidimar ƙasar a jihar Cross River."
Abin da jami'ai da na'urorin NYSC suka gaza ganowa shi ba shi ne, ɗan jarida Umar ya taɓa yin hidimar ƙasa a baya bayan ya kammala digirinsa na farko a Jami'ar Jihar Nasarawa.
"Hakan ya nuna cewa akwai matsala a ɓangaren NYSC saboda na'urorinsu ba su tare wannan matsalar ba," in ji Jaafar.
Mun dakatar da digirin Kwatano har sai an kammala bincike - Gwamnatin Najeriya
Sakamakon wannan rahoto, gwamnatin Najeriya ta ce ta ɗauki matakin dakatar da tantance shaidar karatun digiri daga jami'o'in Jamhuriyar Benin da na Togo.
Cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta Najeriya, Augustina Obilor-Duru, ya ce rahoton ya bayyana hanyoyin da wasu ƴan Najeriya ke bi domin samun takardar shaidar karatun digiri da nufin samun damamrmakin aiki da ba su cancanta ba.
"Ma'aikatar ilimi ta koka da irin wannan ɗabi'a kuma daga ranar 2 ga watan Janairun 2024, ta dakatar da tantance takardun shaidar karatun digiri daga Benin da Togo har zuwa lokacin da za a kammala bincike," in ji shi.
"Binciken zai haɗar da ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya, da ƙasashen biyu, da ma'aikatun da ke kula da ilimi a ƙasashen, da hukumar tsaro ta farin kaya, da hukumar kula da shirin matasa 'yan hidimar ƙasa ta NYSC."
Ma'aikatar ta yi kira ga yan Najeriya su ba da gudunmawa wajen samar da bayanan da za su taimaka wa kwamitin yayin da yake neman hanyoyin magance faruwar haka a gaba.
Ba wannan ne karo na farko da jaridar ta taɓa yin rahoto kan wannan batu ba, in ji Jaafar Jaafar, amma sai yanzu ne gwamnati ta ɗauki mataki kan hakan.
"Da ma buƙatar maje Hajji sallah, idan mutum ya yi ƙoƙarin kawo gyara a cikin al'umma ya tabbata dole zai ji daɗi kuma ya ƙara ƙaimi don ya duba wani ɓangaren da ake samun matsala domin hukumomi su kawo gyara."










