Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu cin zarafin da ke lalata ƙananan yara a filin ƙwallon Gabon
Masu cin zarafin da ke lalata ƙananan yara a filin ƙwallon Gabon
Hukumomin kula da harkar kwallon kafa na fuskantar zarge-zarge a kan gaza kare kananan yara da lalatawa a Gabon.
Sashen Binciken Kwakwaf na BBC a Afirka wato BBC Africa Eye ya zanta da shaidu fiye da 30 wadanda suka yi bayani a kan wani gungun mutane da ya addabi harkar wasanni a dukkan matakai tsawon shekara 30.