Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaya shirin hidimar ƙasa na Najeriya ya canza rayuwarku?
Yaya shirin hidimar ƙasa na Najeriya ya canza rayuwarku?
Dumbin 'yan Najeriya ne ke gasar sanya hotunansu da ke nuna yadda suka yi aikin hidimar ƙasa na tsawon shekara ɗaya a shafukan sada zumunta, daidai lokacin da hukumar kula da aikin hidimar ƙasa ta Najeriya (NYSC) ke cika shekara 50 da kafuwa.
Taken bikin cika shekara 50 ɗin da kafa hukumar shi ne "50: Goma biyar ta kyautata haɗin kai da bunƙasa ci gaban ƙasa".
To, ko yaya shirin ya taimaka wajen bunƙasa rayuwar matasa?