Ƴan sanda sun kama ɗan majalisar wakilai da daloli maƙare a cikin jaka

Dollars

Asalin hoton, RIVERS STATE POLICE COMMAND

Rundunar ƴan sandan jihar Ribas da ke kudancin Najeriya ta ce ta kama wani ɗan majalisar wakilai da kuɗi dalar Amurka kusan rabin miliyan.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, SP Grace Iringe Koko ta fitar, ta ce ta kama Honorabul Chinyere Igwe, ɗan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Port Harcourt II da kudi dalar Amurka a cikin wata jaka a bayan motarsa.

Sanarwar ta ce mataimaki sufeto janar na ƴan sanda, AIG Abutu Yaro ya bayar da umurnin a gudanar da bincike kan lamarin ba tare da ɓata lokaci ba.

“A yau 24 ga watan Fabarairu da misalin karfe uku na dare, ƴan sandan da ke aiki a jihar Ribas a kan hanyarsu ta zuwa shalkwatar hukumar zaɓe – INEC suka tsayar da motar wani kuma suka gano dalar Amurka dubu 498 da ɗari ɗaya a cikin wata jaka a bayan motarsa,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa akwai wata takarda ta yadda za a yi kasafin kuɗin.

...
...

A zaɓukan baya, ana zargin 'yan siyasa da amfani da kuɗi wajen sayen kuri'un jama'a.

A halin yanzu dai ana ƙarancin takardun kuɗi na naira a Najeriya abin da ya jefa 'yan siyasa cikin zullumi game da yadda za su samu kuɗin sayen ƙuri'a.

Rundunar ƴan sandan ta buƙaci dukkan ƴan takara da jam’iyyu siyasa su bi dokokin zaɓe.

Sanarwar ta kuma yi kira ga al’umma su kai ƙarar duk wanda suke tunanin yana ƙoƙarin tayar da zaune tsaye.

Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana guda kafin babban zaɓen Najeriya, inda al'umma za su zaɓi sabon shugaban ƙasa da kuma ƴan majalisar dokokin tarayya.

Honorabul Igwe dai ɗan majalisa ne na jam'iyyar PDP mai adawa a ƙasar.