KU BA MU LABARANKU: Ta yaya ambaliyar ruwa ta shafe ku a bana?

Hukumar Agajin Gaggawa ta Najeriya ta ce mutum 372 ne suka rasa sayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a jihohi 33 da kuma babban birnin tarayyar Abuja a ƴan watannin da suka wuce.

Kazalika ambaliyar ta rusa dubban gidaje da lalata gonaki da amfanin gona a fadin kasar.  Shin kuna cikin mutanen da suka yi rashin ƴan uwa ko dangi sakamakon ambaliyar? Ba mu labarin yadda lamarin ya faru – idan har mun ga labarinku mai ma’ana ne, to za mu tuntuɓe ku don yin hira da ku da kuma wallafa shi.

Ku aiko mana da tsokacinku

Our data policy

A yayin da muke muradin karanta dukkanin sakonnin imel din da kuka aiko mana, ba za mu iya ba ku tabbacin aika muku da amsa ba. Akwai yiwuwar mu aika muku amsar imel din ko mu tuntube ku don karin bayani. Idan da hali, za mu iya gyara bayanan da kuka aiko mu kuma wallafa a shafukanmu na BBC Hausa. Idan ba kwa son a sanya bayananku, to sai ku gaya mana. Ba za mu bai wa duk wanda ba ɗan BBC ba bayananku ba tare da izininku ba.

BBC ce babbar mai kula da bayanan da kuka bayar. BBC za ta sarrafa waɗannan bayanan saboda buƙatarata a matsayita na kafar yaɗa labarai a matsayin shaida. Idan kuna da tambaya a kan yadda BBC ke adana bayananku, ku duba nan don ganin Tsarin Sirrin Na BBC: https://www.bbc.co.uk/usingthebbc/privacy/

BBC za ta adana bayananku har sai zuwa lokacin da aka kammala amfani da su.