Najeriya: Shin dokar dandaƙa ga masu fyade a jihar Kaduna na tasiri?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ishaq Khalid
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Matsalar fyade na ci gaba da kasancewa gagarumar matsala a Najeriya inda kusan a kullum sai an samu labarin yin sa - wasu lokutan kuma kan rutsa da kananan yara.
A watan Yunin shekarar da ta gabata ilahirin gwamnonin jihohin kasar 36 suka ayyana dokar ta-baci kan matsalar fyaden, wadda ta kai ga wasu jihohi sun tsaurara dokokinsu na yaki da fyade.
Ga alama dai jihar da ta fi daukar hankali ita ce jihar Kaduna da ke arewacin kasar sakamakon dokar da gwamnatin jihar ta kafa a watan Satumba ta dandaƙe duk wanda aka samu da lafin yi wa yaro ko yarinya fyade da nufin dakile matsalar.
'Maza 10 sun yi wa 'yar shekara 12 fyade'
Na tarar da marainiya mai shekara 12, Ladidi, wanda ba ainihin sunanta kenan ba, tana zaune kusa da babban yayanta kuma mai kula da ita, tana ta zubar da hawaye. Ta yi gum, ta kasa fada mani abin da ya faru da ita watanni uku da suka gabata.
Amma yayan nata ya yi mani bayani. Ya shaida mani cewa ana zargin wasu maza goma ne suka yi mata fyade cikin watan goma wato Oktoba - makwanni kalilan bayan da gwamnatin jihar Kaduna ta ƙarfafa dokarta ta yaƙi da matsalar fyaɗe.
Sanadin lalatar, ta kamu da ciwon sanyi, ana kuma yi mata magani. Danginta sun kadu, sun dugunzuma, suna kuma dakon adalci ta fuskar shari'a. Mun dai sakaya sunansa domin kada a shaida kanwar tasa.
Cikin takaici, ya ce lamarin ya yi matukar yi masu ciwo a zuci, yana mai cewa ''sun cutar da rayuwar yarinya, kuma sun cutar da mu.'' Sai dai ya kara da cewa a kullum suna kokarin rarrashinta da kuma karfafa mata gwiwa da cewa rayuwarta za ta yi kyau a gaba.
An dai kama takwas daga cikin wadanda ake zargin - sauran biyun sun gudu. Hukumomi na cewa duka za su fuskanci shari'a.
Dan-uwan ''Ladidi'' ya ce wasu daga cikin wadanda suka yi mata fyaden mutane ne da kan yi hulda da gidansu, wannan kuma na daya daga cikin abubuwan da suka girgiza su.
Katutun matsalar ƙyama da tsangawama ga wadanda aka yi lalata da su, da karancin kai rahoton fyade ga hukumomi, da karancin hukunta masu fyaden da kuma jinkiri da sarƙaƙiya ta fuskar tsarin shari'a na daga cikin kalubalen da ake fuskanta wajen daƙile matsalar fyade a Najeriya, a cewar masu sharhi.
Amma yayan Ladidi ya ce fatansu shi ne kotu ta samu wadanda ake zargi da yin lalata da ƙanwarsa da laifi, kuma a hukunta su daidai da sabuwar dokar yaƙi da fyaɗe ta jihar Kaduna - wato a dandaƙe su kuma a zattar masu da hukuncin kisa.

Matsalar fyade ta zama annoba

Kusan a kullum dai sai an samu labarin cewa an yi wa wata ko wani fyaɗe a Najeriya. Kungiyoyi, musamman masu fafutikar kare hakkin mata da kananan yara, na ta yin kumaji da kuma nuna damuwa kan matsalar ta fyade - matsalar da wasu ke cewa ta zama annoba a cikin al'umar kasar.
Ko a cikin shekarar da ta gabata irin wadannan kungiyoyi sun yi ta yin zanga-zanga a tituna a sassa daban-daban na Najeriya domin kara jawo hankalin al'uma da mahukunta ga matsalar.
Yayin da yake da wahala a iya samun takamaiman alkaluma na hakikannin yawan fyade a Najeriya mai jihohi 36, a jihar Kaduna kadai hukumomi sun ce an samu rahotannin lamuran fyade 1,046 daga watan Janairu zuwa watan Nuwamban 2020.
Wannan adadi na nuni da karuwar kamar kashi 50 cikin 100 kan yawan fyade da aka samu rahotanninsu a 2019 a jihar.
Duk da haka an yi imanin cewa akwai lamuran fyade da dama wadanda ba a kai rahotanninsu ga hukumomi ba. Haka zalika ba kasafai ake hukunta masu fyaɗe a kotuna ba.
Wasu kuma cewa su ke yi kamata ya yi a maida hankali ga shawo kan matsalolin dake janyo fyade baya ga kokarin hukunta masu aikatawa.
Hajiya Rabi Salisu Ibrahim wata mai fafutikar yaki da fyade ce. Kungiyarta mai suna Arida Relief Foundation ta bi diddigin lamuran fyade fiye da 500 cikin shekaru biyar da suka gabata - to amma bakwai ne kacal suka kai ga samun hukuncin kotu kan wadanda aka gurfanar.
Ta ce matsalar ba ta sauya doka ko kafa sabuwar doka ba ce, a 'a, ana bukatar daukar karin matakai ne na zahiri wajen aiwatar da dokokin, da kuma ingantawa da hanzarta tsarin gabatar da shaida ko kuma hujjar tabbatar da fyade. Hajiya Rabi ta koka da wahalar da ake fuskanta wajen gabatar da shaida da kuma dawainiya tsakanin hukumomin tsaro da asibiti.
Ta shaida wa BBC cewa wasu daga cikin hujjoji da ake bukata sun hada da tabbatar da cewa lallai akwai saduwa a tsakani, ko alamar rauni ko kuma jini daga wanda ake zargin an yi wa fyade. Mai fafutikar ta ce wannan babban kalubale ne wajen tabbatar da laifi a kotu.
Ta kuma ce sarkakiyar shari'a kan sa wani lokaci shari'ar fyade ta iya daukar ''shekaru 10'' ana yi, kuma irin wannan yanayi kan sanyaya gwiwar wadanda aka yi wa fyade ko kuma iyayensu, har su gaji su ce sun janye daga shari'ar.
Ba a hukunta kowa ba tun bayan kafa dokar dandaka a jihar Kaduna.
Dokar ta jihar Kaduna tana janyo cece-ku-ce musamman batun tanadin hukuncin dandaka ko cire bututun mahiafa da kuma kisa ga wanda ya yi ko ta yi fyade ga yaro ko yarinyar da ba su wuce shekara 14 da haihuwa ba.

Labarai masu alaƙa

Dokar ta kuma tanadi hukuncin dandaka da kuma daurin rai-da-rai idan wadda aka yi wa fyaden ta wuce ko ya wuce shekara 14 da haihuwa.
Amma daya daga cikin hujjoji da ake bukata shi ne sakamakon gwaji na asibitin gwamnati dake tabbatar da cewa an yi lalata da yaron ko yarinyar. A watan Satumban 2020 ne gwamnan jihar Malam Nasir el-Rufai ya sanya hannu a kan dokar bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da ita.
Gwamnatin jihar Kaduna dai ta ce ta kafa dokar ne domin ta kasance ishara ko izina ga masu aikata fyade a jihar saboda yadda fyade ta yi yawa musamman ga kananan yara. Dokar ta sha yabo daga masu fafutikar yaki da fyade inda wasu suka yi fatan zata tsorata masu fyade - musamman idan aka aiwatar da hukunci.
Haka nan mutane da dama sun ce kafa dokar ya taimaka wajen kara bayyana girman matsalar fyade da kuma bukatar daukar mataki.
Amma wasu na ganin ba a nan gizo ke saka ba. Kwamishinar kare hakkin bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Michelle Barchellete, ta ce akwai mugunta cikin dokar, kuma tamkar neman magance ɓarna ce da wata ɓarnar. Ta kara da cewa dokar ta keta hakkin-Adama.
To sai dai tun da dokar ta jihar Kaduna ta soma aiki cikin watan Satumba, kawo yanzu, kotu bata samu wani da laifin fyade bisa tanade-tanaden dokar ba, balle a yi batun dandake shi ko hukuncin kisa, ko kuma cire bututun mahaifa.
Haka kuma kawo yanzu babu alamar adadin fyade da ake yi a jihar ya ragu bayan kafa dokar.

Asalin hoton, Hafsat Baba
To amma kwamishinar Ayyukan Kyautata Rayuwar bil-Adama da Zamantkewa ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, ta ce ya yi wuri a yanke hukunci kan tasiri da ingancin dokar - kasancewar watannni kalilan ke nan da aka kafa ta.
Hajiya Hafsat Baba ta shaida wa BBC cewa lallai jihar Kaduna ta na kan kyakkyawar turba ta magance matsalar fyade kuma a cewarta, mutane na farin ciki da dokar.
Kwamishinar ta jihar Kaduna ta ce shari'a na da tsarinta kuma dole a bi tsarin kafin a kai ga yanke hukunci da kuma zattas da hukunci.
Ta bayar da tabacin cewa da yardar Allah za a aiwatar da dokar a kan duk wanda aka samu da laifi, kuma yanzu hukumomi na tsare-tsaren yadda za a rika hanzarta yin shari'o'in fyade a jihar.
Dangane da zargin da wasu ke yi na cewa dokar ta yi tsanani kuwa, jami'ar ta ce ''Da wannan doka ta fito, masu korafi a kanta, sai muka ga kamar sun fi tausaya wa wanda ya yi fyade, fiye da wanda aka yi wa fyaden, ko namiji ne ko tamace.''
Ta kara da cewa akwai bukatar kare hakkin wadanda aka yi wa fyade domin duk wanda aka yi wa fyade an yi wa rayuwarsa illa kuma ''hatta iyaye da 'yan-uwansa'' za su shiga ''wani hali.''
Sai dai masu fafutika irinsu Hajiya Rabi Ibrahim na nuna bacin ransu kan rashin hukunci tun bayan kafa dokar ta jihar Kaduna. Ta bayyana fargabar cewa muddin ba a yin hukunci, to za a ci gaba da fuskantar ayyukan fyade a cikin al'uma.
Wani batu da hukumomi da kuma masu fafutika ke kokawa a kai shi ne yadda masu unguwa ko kuma 'yan uwan yaran da aka yi wa fyade kan yi kokarin sasanta matsalar a gida ba tare da an kai ga hukuma ba - wasu lokutan da sunan cewa matsala ce ta cikin gida da kuma gudun ''abin kunya'' idan maganar da fita waje.
A wasu lokuta kuma ana zargin amfani da kudi wajen kashe wutar maganar musamman idan wanda aka zalunta mai karamin karfi ne.
Amma jihohi da dama na sauya dokokinsu domin mayar da laifin fyade ya kasance babban laifi wanda ko iyaye da 'yan uwa sun janye daga maganar, gwamnati na da hakkin bin kadin wanda aka yi wa fyade da kuma hukunta wanda ya aikata. Jihar Kaduna na cikin irin wadannan jihohi.
Yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ku ce kan tasirin dokar ta fyade a jihar Kaduna, su kuwa wadanda aka yi wa fyade kamar marainiya ''Ladidi'', da danginsu, na fatan watan wata-rana za a yi masu adalci, a hukunta wadanda aka samu da laifin zaluntarsu.

Wadanda aka yi wa fyade na bukatar kulawa
Yayan marainiya 'yar shekara 12 da ake zargin an yi mata fyade wato ''Ladidi'' ya ce tun bayan faruwar lamarin ba ta da sukuni a rayuwarta.
Ya ce kafin faruwar lamarin, Ladidi yarinya ce mai kazar-kazar da walwala, amma yanzu ''sai ka same ta ta zauna ta yi shiru tana da tunani'' kuma ba ta cika shiga cikin sauran yara tana wasa kamar yadda ta saba ba.
Masana na bayyana irin wannan yanayi a matsayin daya daga cikin manyan alamomi na tsananin damuwa a rayuwa da kan shafi tunani da kwakwalwar mutum.
Wata kwararriya kan tunani da halayyar bil-Adama, Dakta Fatima Akilu, ta shaida wa BBC cewa yayin da hukumomi ke ta kokarin kafa dokoki da kuma hukunta masu aikata fyade, yana da muhimmanci a mayar da hankali wajen taimaka wa wadanda aka yi wa fyade ta fuskar gyara rayuwarsu da kuma tunaninsu.
Ta ce ''wadanda aka yi wa fyade na bukatar taimako'' saboda fyade kan gigita rayuwar duk wanda aka yi wa - imma namiji ko ta mace. Ya kamata a kafa cibiyoyin bai wa wadanda aka yi wa fyade shawarwarin kwararru a Najeriya, inji Dokta Fatima.
Kwamishinar Ayyukan Kyautata Rayuwar bil-Adama da Zamantakewa ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Baba ta ce yanzu haka akwai cibiyoyi hudu na kula da wadanda aka ci zarafinsu a jihar Kaduna inda ake yin gwaje-gwajen likita, da ba su taimako ta fuskar lafiya da kuma shawarwarin kwararru ta fuskar tunani da kuma rarrashi.
A bangare guda kwararriya Dr Fatima Akilu ta ce dole ne a kara horar da alkalai da lauyoyi da kuma masu fafutika kan yadda za a inganta tattaro hujjoji da shaidu ta hanyar kimiya domin a samu nasara idan aka kai kara a kotu kan matsalar fyade.
Sai dai ta ce ko da yake yin hukunci ga wadanda suka aikata fyade na da matukar muhimmanci wajen magance matsalar a cikin al'umma, amma hukunci ba shi ne kadai matakin magance matsalar fyade ba, sai an hada da daukar wasu matakan.
Mutane da dama na kallon cewa neman biyan bukatar jima'i ne ke ingiza wasu su aikata fyade, amma wasu masu sharhi na cewa ba sha'awar jima'i ce kadai ke sa wasu aikata fyade ba.
Akwai wasu dalilan da suka shafi tunaninsu da kwakwalwarsu, imma neman huce wani haushi ko kuma wani dalilin na daban kamar tsafi.
Dokta Fatima ta ce mai da himma wajen yin nazari kan dalilan da kan sa mutane su aikata fyade, shi ma yana da muhimmanci da nufin dakile su musamman ganin yadda a cewarta yanzu matsalar fyade ''ta yi katutu cikin al'umma.''











