Ko za ku iya banbance fuskar gaske da wadda aka haɗa da AI?

Asalin hoton, ANU (left; generated using StyleGAN3) / Igor Alecsander via Getty Images (right)
- Marubuci, Catherine Heathwood
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Babu wani abu da ya nuna akwai matsala lokacin da wani ma'aikacin harkokin kuɗi a Hong Kong ya shiga taro da abokan aikinsa suka gudanar ta bidiyo a kamfanin injiniyanci na Arup domin tattauna wani sirrin saye da haɗewar kamfanoni a shekarar 2024.
Sai bayan ya tura kuɗi har dala miliyan 25 ne ya gano cewa an yaudare shi. Duk sauran mutanen da suke cikin kiran bidiyon, har da wanda ya yi kama da babban jami'in kuɗi na kamfanin , hotunan ƙirƙira ne da aka samar ta amfani da fasahar AI ta "deepfake".
Fuskokin da AI ke ƙirƙira suna ƙara wahalar bambancewa da na mutane na gaske. A cewar wani rahoto da kamfanin ba da shawara na Deloitte ya fitar a shekarar 2024, ana hasashen cewa damfarar da ake yi ta amfani da AI mai samar da bayanai da hotuna za ta jawo asarar dala biliyan 40 a Amurka kaɗai nan da shekara mai zuwa.
Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Farfesa Amy Dawel, ƙwararriyar masaniyar ilimin halayyar ɗan Adam a Jami'ar Ƙasa ta Ostiraliya (ANU), ta so ta gano ko za a iya horas da mutane su fi iya gane fuskokin da AI ya ƙirƙira.
"Yanzu muna da matuƙar rauni wajen gane fuskokin da AI ya ƙirƙira." Ta ƙara da cewa bincike ya nuna cewa ƙwarewarmu wajen gane su ba ta kai ko da kaso 50 a cikin 100 ba kuma wasu lokuta ma ta fi haka muni.
To, kai fa? Yaya ƙwarewarka take wajen bambance fuskar da AI ya ƙirƙira daga fuskar mutum ta gaske?
Fuskoki masu kama da na ɗan'adam
Idan ka sha wahala wajen yin gwajin da ke sama, ba kai kaɗai ba ne.
Amy Dawel ta ce wahalar gane fuskar da AI ya ƙirƙira na da sakamako na gaske da ke shafar kowa da kowa, "ko dai ta hanyar yaudarar soyayya a intanet , ko a shafukan neman abokan zama, ko kuma hare-haren da ake kai wa asusunmu na banki."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wani bincike da aka wallafa a watan Yuni a mujallar kimiyya ta PNAS, Dawel da abokan aikinta daga Ostiraliya, Kanada da Scotland sun gwada wata sabuwar hanya ta horar da mutane.
Yayin da fasahar AI ke ƙara inganta, sabbin tsare-tsarenta sun riga sun gyara yawancin kurakuran da aka saba gani a baya.
Dawel ta ce masu damfara ba su da yiwuwar amfani da hotunan da ke ɗauke da irin waɗannan kurakurai.
Maimakon koya wa mutane su rika neman alamomin kuskure da ke bayyana AI, kamar 'yan kunne da ba su yi daidai ba ko siffofin fuska da suka karkace, masu binciken sun horar da su su yi amfani da hasashen farko da fahimtar da suke samu game da fuskar gaba ɗaya.
Dawel ta ce: "Daya daga cikin matsalolin shi ne muna tsammanin fuskokin da AI ta ƙirƙira za su kasance baƙaƙe ko marasa daidaito, saboda abin da muka gani a baya.
Amma a zahiri mutane ne ba su da cikakkiyar daidaito a fuskokinsu kuma suna da wasu siffofi na musamman. Saboda haka, yanayin ya juya gaba ɗaya."

Asalin hoton, JohnnyGreig via Getty Images (left) / seb_ra via Getty Images (right)
Wani bincike da Dawel da tawagarta suka yi a baya ya gano cewa mutane sun fi yarda cewa fuskokin da AI ya ƙirƙira na mutane ne na gaske fiye da ainihin fuskokin mutane. Sun ba wannan al'amari suna "AI hyperrealism" wato "Ƙirƙirar fuskoki masu kama da gaskiya fiye da gaskiya ta hanyar AI"
Dawel ta ce tun da tsarin AI na ƙirƙirar hotuna yana dogara ne kan matsakaicin siffofi daga dubban fuskoki da aka horas da shi da su, "fuskokin da AI ke ƙirƙirawa suna kama da matsakaiciyar fuska, ko ma fiye da matsakaiciya, idan aka kwatanta da fuskokin mutane na gaske."
Ta ce wannan yana sa irin waɗannan fuskoki su bayyana kamar:
- Sun fi zama abin amincewa,
- Sun fi jan hankali,
- Kuma suna ba mutane jin kamar sun saba da su, fiye da yadda ainihin fuskokin mutane ke yi.
Sai dai, binciken ya mayar da hankali ne kawai kan fuskokin fararen fata da AI ya ƙirƙira.
Yawancin tsarin AI yana horas da su ne da hotunan fararen fata fiye da na sauran ƙabilu, saboda haka akwai yiwuwar irin waɗannan fuskoki su bayyana a matsayin na gaske sosai idan aka kwatanta da fuskokin wasu jinsuna ko ƙabilu.
Bincike
A sabon binciken, tawagar masana ta fara ne da gwada yadda manya 45 za su iya gane fuskar da AI ya ƙirƙira kafin a ba su horo.
A cikin wani gwaji, an nuna musu fuskoki uku a lokaci guda, sannan aka nemi su zaɓi wacce AI ya ƙirƙira. A taƙaice sun dace a kashi 41 cikin 100 na lokuta.
Daga nan aka ba mahalarta horo na kusan awa guda. Dawel ta ce horon ya haɗa da nuna musu kusan fuskoki 100 — rabinsu na mutane na gaske, rabinsu kuma ƙirƙirar AI — sannan aka nemi su tantance kowace fuska bisa halaye shida gaba ɗaya:
- Bambantuwa (distinctiveness)
- Sauƙin tunawa da ita (memorability)
- Bayyana motsin rai (expressiveness)
- Daidaiton sassa (symmetry)
- Daidaituwar gwargwado (proportionality)
- Kyawu ko jan hankali (attractiveness)
A cewar Dawel, fuskokin mutane na gaske sun fi kasancewa na musamman, masu sauƙin tunawa da kuma nuna motsin rai.
A gefe guda kuma, fuskokin da AI ya ƙirƙira sukan fi daidaito, gwargwado da kuma jan hankali.
"Ba ma gaya musu cewa fuskokin AI sun fi daidaito. Abin da kawai suke yi shi ne tantance matakin daidaiton fuskar. Ana gaya musu ko fuskar ta AI ce ko ta mutum, kuma ta hanyar wannan maimaita gani suna fara fahimtar bambance-bambancen da ke tsakanin fuskokin AI da na mutane."
Bayan horon, mahalarta binciken sun kusan ninka ƙwarewarsu wajen gane fuskokin AI. Matsakaicin nasararsu ya tashi zuwa kashi 81 cikin 100 a gwajin da aka ambata a sama.
A matsayin ci gaba ga wannan bincike, wasu abokan aikin masu binciken a Kanada sun gudanar da irin wannan horo ga wata ƙungiyar masu sa kai daban.
"Sun nazarci bayanan su daban, kuma sun gano irin wannan gagarumar fa'ida da sakamako mai ƙarfi," in ji Dawel
Yadda mutane ke ganin abubuwa
Dr Alejandro Estudillo, wani masanin ilimin halayyar ɗan Adam da ke binciken yadda mutane ke fahimtar abubuwan gani a Jami'ar Bournemouth ta Birtaniya, wanda bai shiga cikin wannan binciken ba, ya shaida wa BBC cewa ya yi mamakin abin da ya karanta a binciken.
Ya ce hakan ya ba shi mamaki ne saboda sakamakon binciken ya saɓa wa hanyoyin da sauran masu bincike suka saba amfani da su wajen koyar da mutane yadda za su gane hotuna ko fuskokin da AI ya ƙirƙira.

Asalin hoton, JONATHAN NACKSTRAND/AFP via Getty Images
Amma ya ce abin da ya sa wannan sabuwar hanyar ta zama ta musamman shi ne yadda take amfani da fahimtar da mutane ke da ita a dabi'ance.
"Mutane ba sa nazarin fuska ta hanyar mai da hankali kan sassa ɗaya-ɗaya. Maimakon haka, muna amfani da abin da ake kira 'holistic processing', wato yadda muke haɗa dukkan siffofin fuskar gaba ɗaya domin mu gane ta cikin sauƙi," in ji shi.
Ya ce, misali, idan aka nemi mutum ya tantance yadda fuska take da bambanci ko kuma yadda take daidaito, ba zai mayar da hankali kan wani ɓangare guda na fuskar ba. Dole ne ya dubi fuskar gaba ɗaya.
"Babu wanda ya yi tunanin cewa watakila hanya mafi inganci ita ce a bar mahalarta su nazarci fuskoki ta hanyar da suke yi a rayuwarsu ta yau da kullum," kamar yadda Estudillo ya yi ƙarin haske.
Ƙalubale da iyakoki
Sai dai binciken yana da wasu ƙalubale da iyakoki.
Dawel ta ce an tabbatar da cewa horon yana da matuƙar tasiri wajen gano fuskokin da ɗaya daga cikin mafi ingancin tsarin ƙirƙirar fuskokin AI, wato StyleGAN3, ya samar. Amma har yanzu ana buƙatar gwada shi a kan sauran nau'ukan tsarin AI.
"Dukkan mahalartan bincikenmu matasa ne. Don haka akwai muhimman tambayoyi kan ko wannan horo zai yi tasiri ga yara ko tsofaffi, waɗanda muka sani cewa su ma suna cikin rukunin da masu damfara ke yawan kai wa hari."
Masu binciken sun ce babban ƙalubalen shi ne cewa yanzu mutane suna fafatawa da tsarin AI da ke ci gaba da inganta kansa a koyaushe.
Akwai wasu kayan aiki da ke amfani da lissafin kwamfuta (algorithms) wajen gano abubuwan da AI ya ƙirƙira. Amma waɗannan kayan aikin ma suna da nasu gazawar.
Sau da yawa suna aiki ne kawai da wasu nau'ikan AI, kuma suna iya fuskantar matsala idan sabbin nau'ukan AI sun bayyana ko kuma an yi wa hotuna gyare-gyare. Saboda haka, masu binciken sun ce yana da muhimmanci a ci gaba da dogaro da mutane wajen gano hotuna, bidiyo da sautukan da aka samar ta hanyar ƙirƙirar basira ta "deepfake".
"Wannan kamar wasan mage da ɓera ne. Yana kama da ƙwayoyin cutar kwamfuta da ake kira da computer viruses da ke ci gaba da canzawa, yayin da mu ma dole ne mu ci gaba da sabunta hanyoyinmu domin mu iya bin su."
Duk da haka, ta yi imanin cewa sakamakon binciken ya ba da "kyakkyawan dalilin yin fata."
Ta ba da shawarar cewa nan gaba za a iya samar da irin wannan horo domin taimaka wa mutane wajen gano sautuka da bidiyoyin da AI ya ƙirƙira, ba fuskoki kaɗai ba.
Hakan na iya sa mu duka mu kasance cikin shiri mafi kyau wajen gane ko mutumin da muke magana da shi a wani kiran bidiyo abokin aikinmu ne na gaske, ko kuma na gangan ne na basirair "deepfake" da AI ya ƙirƙira ne.












