Likitan da ya kamu da Ebola ya warke

Asalin hoton, Getty
Likitan nan Ba amurke da ya kamu da cutar Ebola a Liberia ya warke kuma an sallame shi daga asibiti a Amurka.
An bai wa Dr. Kent Brantly maganin Zmapp da ake gwajin shi a lokacin da ake kula a wani asibiti da ke jihar Atlanta ta Amurka.
Hakan na zuwa ne yayin da wasu likitoci uku da suka kamu da cutar a Liberiya ke ci gaba da samun sauki, bayan an ba su maganin na Zmapp.
Sai dai kamfanin da ya hada maganin ya ce a yanzu babu sauran maganin da ya rage.






