Ebola: Kasuwar naman Biri ta yi kasa a Nigeria

A Najeriya mutane na kauracewa wuraren da ake sayar da naman Biri da barewa da jemage da dangoginsu sakamakon bullar cutar Ebola a kasar.
Hakan ya sa kasuwar irin wadannan nama ta yi kasa sosai a sassa daban-dabn na kasar.
A baya dai mutane da dama ne ke zuwa irin wadannan wurare, bayan sun tashi daga aiki ko kuma a ranakun Asabar da Lahadi domin cin naman irin wadannan dabbobi da kuma shan barasa.
Kawo yanzu dai mutane biyar ne hukumomi suka tabbatar sun mutu sakamakon cutar Ebola a Najeriya, yayin da ake ci gaba da yunkurin hana bazuwar cutar.








