Nigeria za ta kawar da ta'addanci ta lalama

Kanar Sambo Dasuki

Asalin hoton, The Will

Bayanan hoto, Wasu na ganin amfani da lalama zai taimaka wajen magance matsalar Boko Haram a Najeriya

Ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro ya fito da wani shiri na amfani da lalama wajen kawar da ta'addanci a kasar.

Mai bai wa shugaban kasar shawara, Kanar Mohammed Sambo Dasuki ya ce za su hada gwiwa da bangarorin al'umma, domin hana mutane zama 'yan ta'adda a maimakon magance matsalar bayan ta faru.

Kanar Dasuki ya yi nuni da cewa yana da wuya a tantance 'yan ta'adda da wanda babu ruwansu, abin da ke sa wa a wasu lokutan, matakan soji kan shafi wanda bai ji ba bai gani ba.

Sau da dama dai ana zargin jami'an tsaro wajen wuce gona da iri a yunkurin kawar da 'yan ta'adda a kasar.