Ba a fahimce mu kan batun tace fina-finan YouTube ba - Afakallah
Danna hoton sama domin kallon bidiyon
Shugaban hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano Malam Ismail Naabba Afakallah ya ce mutane sun yi musu mummunar fahimta kan batun cewa sai an tantance fina-finan Hausa da ake sa wa a YouTube.
Malam Isma'ila Afakallah ya ce dokar za ta yi aiki ne kawai kan fim din da aka yi a Kano, ko kuma wanda ya yi fim din ya yi rijista da hukumar tace fina-finai ta Kano.
Shugaban ya kuma ce ba ya nadamar daukar duk wani mataki a matsayinsa na shugaban hukumar ta tace fina-finai ta Kano.
Ya kara da cewa ba shi da matsala da kowa a Kannywood, amma ba za su lamunci raini da keta doka ba.