Ramadan 2022: Abubuwa 11 da suka kamata mai azumi ya mayar da hankali a kai

Latsa wannan alamun hoton da ke sama domin kallon jawabin:

Sheikh Jabir Maihula wanda malamin addinin Musulunci ne a Najeriya ya ce lissafa wasu abubuwan da ya ce ya kamata duk mai azumi ya mayar da hankali a kansu.

Ya ce "ma'anar azumi ita ce barin cin abinci da shan abinsha da kuma barin jima'i daga lokaci kafin fitowar alfijiri zuwa faduwar rana."

Sai dai kuma malamin ya yi karin haske dangane da wasu abubuwa da ya ce masu azumi na yin ganganci yayin da suke yin su.