Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyin da muke bi wajen tantance ganin jinjirin watan Ramadan - Wazirin Sokoto
Latsa wannan alamar hoton da ke sama domin kallon wannan hira
Kwamitin duban wata na Najeriya ya umarci ƴan kasar da su fara duban jaririn watan azumin Ramadan daga ranar Juma'a, wadda ita ce 29 ga watan Sha'aban.
Shugaban Kwamitin, Farfesa Sambo Waliy Janaidu, Wazirin Sokoto ya shaida wa BBC cewa, idan ba a ga jinjirin watan ba ranar Juma'a to za a tsimaye shi ranar Asabar.
"Idan kuma ba a gan shi ba a ranar Juma'a, to kai tsaye Lahadi ce za ta kasance 1 ga watan azumin Ramadana," in ji Waziri.
Farfesa Sambo ya lissafa wasu hanyoyi da suke bi wajen tabbatar da ganin wata kamar haka: