Dalilai hudu da suka sa Koriya ta Arewa take yawaita gwajin makamai masu linzami

Latsa hoton da ke sasma domin kallon bidiyon:

Koriya ta Arewa ta harba haramtaccen makami mai linzami, mai tafiyar dogon-zango a karon farko tun 2017, a cewar Koriya ta Kudu da Japan.

Amma me ya sa shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, yake ci gaba da karya dokokin Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar gwada sabbin makamai lamarin da ya sa aka kakaba mata takunkuman karya tattalin arziki?