Mai shekara 25 da ya zama shugaban matasan jam'iyyar PDP

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani abu mai kama da na al'ajabi da ya faru a taron PDP shi ne yadda aka zaɓi matashi ɗan shekara 25 a matsayin shugaban matasa na PDP.

Ɗan asalin Jihar Kaduna, Muhammed Kadade Suleiman ne matashi mafi ƙarancin shekaru da aka zaɓa a wannan muƙami a matakin ƙasa.

Muƙamin nasa na shugaban matasa na cikin waɗanda aka kaɗa ƙuri'a a kansu sakamakon kasa sasantawa da aka yi tsakanin 'yan takarar.

Shakka babu matasan Najeriya za su zuba ido don yin koyi da shi yayin da zai jagorance su a PDP zuwa babban zaɓe na 2023.