Mai shekara 25 da ya zama shugaban matasan jam'iyyar PDP

Bayanan bidiyo, Mai shekara 25 da ya zama shugaban matasan jam'iyyar PDP

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani abu mai kama da na al'ajabi da ya faru a taron PDP shi ne yadda aka zaɓi matashi ɗan shekara 25 a matsayin shugaban matasa na PDP.

Ɗan asalin Jihar Kaduna, Muhammed Kadade Suleiman ne matashi mafi ƙarancin shekaru da aka zaɓa a wannan muƙami a matakin ƙasa.

Muƙamin nasa na shugaban matasa na cikin waɗanda aka kaɗa ƙuri'a a kansu sakamakon kasa sasantawa da aka yi tsakanin 'yan takarar.

Shakka babu matasan Najeriya za su zuba ido don yin koyi da shi yayin da zai jagorance su a PDP zuwa babban zaɓe na 2023.