Songhai: Yadda 'Afirka ke fitar da arzikinta tana shigar da talauci'

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wannan labari ne na wani haifaffen Najeriya Father Godfrey Nzamujo wanda matsalar fari da yunwar da aka yi fama da ita a Habasha a shekarun 1980 ta zaburar da shi.

Wannan abu ne ya sanya masa azama, kuma a shekarar 1985 ya ƙirƙiri tsarin Songhai - wani tsari na alkinta komai da ya danganci harkar noma a Jamhuriyyar Benin.

Ƙasashe da dama kamar su Laberiya da Uganda da Najeriya da kuma Saliyo - sun bi irin wannan tsari na Songhai .