Songhai: Yadda 'Afirka ke fitar da arzikinta tana shigar da talauci'

Bayanan bidiyo, Yadda 'Afirka ke fitar da arzikinta tana shigar da talauci'

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wannan labari ne na wani haifaffen Najeriya Father Godfrey Nzamujo wanda matsalar fari da yunwar da aka yi fama da ita a Habasha a shekarun 1980 ta zaburar da shi.

Wannan abu ne ya sanya masa azama, kuma a shekarar 1985 ya ƙirƙiri tsarin Songhai - wani tsari na alkinta komai da ya danganci harkar noma a Jamhuriyyar Benin.

Ƙasashe da dama kamar su Laberiya da Uganda da Najeriya da kuma Saliyo - sun bi irin wannan tsari na Songhai .