Muhammad Sagir: Matashin da ke kera motar kwali ta wasan yara a Kano
Ku latsa alamar hoton da ke sama domin kallo
Muhammad Sagir, mai shekara 18, ya kammala makarantar sakandare inda ya kware a fannin kasuwanci.
Sai dai Muhammad ya kasance yana zana tare da kera motocin wasa na yara, inda yake amfani da kwalaye.
Wannan matashi, wanda ya ce burinsa yanzu shi ne zama mai kera jirgin sama, ya kasance yana yi wa mahaifiyarsa tallar gwanjo.
"Ina yin tallar gwanjo gida-gida domin sama wa mahaifiyata abin da za ta rike ni da sauran 'yan uwana," in ji shi.
Muhammad kan yi tallar gwanjo daga ranar Alhamis zuwa Juma'a, inda kuma yake halartar makarantar EngHausa domin ci gaba da daukar darussan fasaha da kimiyya a cikin harshen Hausa.
Makarantar EngHausa dai wani wuri ne da ake koyar da matasa harkar fasahar zamani da harshen Hausa da Ingilishi domin saukaka musu fahimtar darasi kamar yadda shugaban wurin ya shaida wa BBC.
"Muna zakulo yara masu fasaha irin Muhammad mu shigo da su wannan makaranta domin koyar da su abubuwan da watakila za su wahala wajen fahimtarsu idan da harshen Turanci kawai aka koya musu."