Murtala Abdulrahman: Matashin da ya kera jirgin sama a Kaduna
Kalli bidiyon matashin da ya kera jirgin sama a Kaduna:
Murtala Abdulrahman wani matashi ne dan asalin jihar Kaduna da ya kera jirgin sama.
A tattaunawarsa da BBC Hausa, ya ce tun yana karamin yaro yake sha'awar kere-kere.
"Tun ina karami nake da ra'ayi na kere-keren abubuwa daban-daban: irin kera motoci su kayan wasa tun muna yata, to abin da ya ja hankalina kenan na ce bari zan gwada na gani ko kera jirgi mai yiwuwa ne," a cewarsa.