...Daga Bakin Mai Ita tare da Teemah Yola, Rukayya ta Labarina

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 58, shirin ya tattauna da Teemah Yola, Rukayya ta Labarina Series, kuma jaruma a Kannywood.

A wannan shiri ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta da rawar da take takawa a masana'antar fina-finai.

Ɗaukar bidiyo: Abdulsalam Usman Abdulkadir

Tacewa: Yusuf Yakasai

Tsarawa da gabatarwa: Buhari Fagge