...Daga Bakin Mai Ita Tare da Hamisu Breaker
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.
A wannan kashi na 38, shirin ya tattauna da fitaccen mawakin nan na Hausa wato Hamisu Breaker Dorayi, inda ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa.
Ya amsa tambayoyi a kan yadda aka yi ya fara waka da kuma sirrin nasararsa.
Ɗaukar bidiyo: Bashir Idris
Tacewa: Abdulsalam Usman Abdulkadir
Tsarawa: Umar Rayyan