...Daga Bakin Mai Ita Tare da Abba El-Mustapha
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.
A wannan kashi na 34, shirin ya tattauna da fitaccen Dan wasan fina-finan Kannywood Abba El-Mustapha inda ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa.
A cikin hirar ya yi karin bayani a kan halayyar da ya fi so da wacce ba ya so, da abin da yake faranta masa rai da ire-iren abincin da ya fi so.
Ɗaukar bidiyo: Yusuf Yakasai
Tacewa: Fatima Othman