APC na sabunta rijista ne saboda an gano wasu sun mayar da rumbun bayanan jam'iyyar Lagos - Abdulaziz Yari

Latsa hoton dake sama domin kallon hirar:

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya ce APC ta ɗauki matakin sabunta rijistar ƴan jam'iyyar ne bayan gano cewa an mayar rumbun bayanan rijistar ƴan jam'iyyar na intanet zuwa Legas.

Abdulaziz Yari - wanda kuma tsohon shugaban ƙungiyar gwamninin Najeriya ne - ya ce tun 2018 suka gano cewa bayanan ba sa babban ofishin jam'iyyar da ke Abuja.

Ya ce wataƙila rashin fahimta ce ta sa tsohon gwamnan na Legas, kuma jagoran APC Na ƙasar Bola Ahmad Tinubu yake adawa da sabunta rijistar.