Binciken Africa Eye: Rayuwar mace mai zaman kanta a matsayin uwa kuma 'ya a Saliyo

Bayanan bidiyo, bidiyon Binciken Africa Eye kan rayuwar mata masu zaman kansu a Saliyo

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mata masu zaman kansu a Saliyo yawanci ana yi musu kallon marasa tarbiyya, la'anannu kuma waɗanda ake gudu da ƙyamata, duk da cewa sana'arsu halastacciya ce a tsarin ƙasar.

Sashen binciken ƙwaf na BBC Africa Eye ya bankaɗo yadda ake cin zarafin mata masu zaman kan nasu a ƙasar, inda kuma ake safararsu har ma da kashe su a wasu lokutan.

Kuma kamar yadda Tyson Conteh ya ruwaito daga garin Makeni, a arewacin Saliyo, rayuwar mata masu zaman kan nasu ta sake tsanani tun bayan ɓullar annobar cutar korona.

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla