Bidiyo: Matan da suka kirkiri lantarki mai amfani da hasken rana na farko a Yemen
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wasu mata a yankin Abs na ƙasar Yemen sun samar da tashar da ke bayar da lanatarki ta amfani da hasken rana – irin ta ta farko a ƙasar.
An samar da shirin ne a shekarar 2019 da taimakon Shirin Samar da Ci gaba da Majalisar Ɗinkin Duniya UNDP.
A yanzu matan sun mayar da tashar lantarki harkar kasuwancinsu, inda suke samar da makamshi mai ɗorewa ga al’ummar da ke zaune kusa da yankin da ake yaƙin basasar ƙasar.