Covid-19: Gargadi ga masu kin sanya takunkumi a Najeriya
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Hukumomi a Najeriya sun wajabta sanya takunkumi a bainar jama'a sakamakon ci gaba da yaduwar cutar korona.
Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince a ci tarar duk mutumin da aka samu da laifin kin sanya takunkumin.
Tuni hukumomi a Abuja babban birnin kasar suka soma cin tarar masu karya wannan dokar.
Cutar korona na ci gaba da yaduwa a kasar, lamarin da ya sa hukumomi suke gargadin mutane kan hadarin kamuwa da ita.
Wannan bidiyon ya yi bayani kan wannan batu.