Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus a Indiya: Garin da aka yi musu makaranta ta farko albarkacin cutar korona
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A lokacin da Santosh ya isa kauyen Neelam Thogu a cikin wani surkuki a jihar Telangana ta Indiya, ya tarar da mutane cikin tsananin talauci kuma ba sa zuwa makaranta.
Ya je garin ne tare da abokansa don kai musu taimakon abinci da magunguna a lokacin da ake cikin dokar kullen annobar cutar korona.
Amma a karshe sai suka zauna a garin suka yi musu makaranta inda suke koyar da yara cikin harshen Turanci da yaren garin Telugu.