Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa Buhari ba ya yi wa 'yan Najeriya jawabi - Garba Shehu
Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Jami'i mai taimaka wa Shugaban Najeriya a kan yada labarai Garba Shehu, ya bayyana wa BBC dalilin da ya sa shugaban ba ya yawan gabatar jawabi kan annobar korona ga 'yan Najeriya.
Garba Shehu ya ce abin da ake bukata shi ne a yi abin da ya kamata ba yawan surutu ba.
Mai taimaka wa shugaban ya ce abin da ya sa Buhari ba ya yawan magana saboda gudun kuskure.
Kalli wannan bidiyon domin ganin cikakken bidiyon.