Nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba nine Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke yi muku sai da safe.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ronaldo ya ci kwallo 125 a Champions League
Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 125 a wasa 161 da ya yi a gasar Champions League.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Za su buga wasa na biyu na daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai ta Champions League tsakanin Manchester United da Barcelona da fafatawa tsakanin Ajax da Juventus ranar 16 ga watan Afirilu.
Man Utd 0-1 Barcelona
Za ku iya auna kokarin 'yan wasan kan rawar da kowanne ya taka latsa nan Manchester United da Barcelona za ku iya yin hakan kafin minti 30 bayan da aka tashi wasa
An tashi wasa Man Utd 0-1 Barcelona
An tashi wasa Ajax 1-1 Juventus
Man Utd 0-1 Barcelona
Har yanzu dai Manchester United ba ta buga kwallo ta nufi raga ba
Kawo yanzu dole United ta ci kwallo idan ta je Nou Camp a wasa na biyu ranar 16 ga watan Afirilu.
Ajax 1-1 Juventus
Dan wasan Juventus wanda ya shiga fili daga baya Douglas Costa ya wuce dan wasa daya ya buga kwallo sai dai ta bugi turke.
Man Utd 0-1 Barcelona
Lionel Messi ya yi bugun tazara kwallo ta bugi kafafuwan katangar United, kuma cikin ruwan sanyi David de Gea ya kama kwallo.
Man Utd 0-1 Barcelona
Sergi Roberto na tabuka wa tun shigarsa karawar yana ta wataya wa kamar yadda yaga dama, Barcelona ta samu bugun tazara irin wajen da Messi ke cin kwallo.
Ajax 1-1 Juventus
Ajax ba ta sa'a a karawar nan, wanda ya shiga fili daga baya Jurgen Ekkelenkamp ya kai hari mai kyau raga, amma kuma Wojciech Szczesny ya hana ta shiga raga.
Man Utd 0-1 Barcelona
Lionel Messi ya karbi kwallo sai dai McTominay ya tokare shi domin hana dan wasan motsa wa ya kuma amfana da hakan.
Man Utd 0-1 Barcelona
Jesse Lingard ya karbi katin gargadi lokacin da ya taba Arturo Vidal, kuma a kusa da Luca Rocchi.
Man Utd 0-1 Barcelona
Diogo Dalot, wanda yake buga wasa ta gefe mafi lokaci ya fita, an kuma maye gurbinsa da Jesse LIngard.
Man Utd 0-1 Barcelona
Har yanzu babu wani kwallo da Manchester United ta buga ta nufi raga.
Man Utd 0-1 Barcelona
Romelu Lukaku ya fita, inda Anthony Martial ya canje shi, kuma an yi masa tafi a filin yadda ya kamata.
Sai dai Lukaku shi ne wanda yake da karancin taba kwallo a karawar.
Man Utd 0-1 Barcelona
Dan wasan Barcelona Sergi Roberto da kuma Arturo Vidal sun shiga fili, inda aka canmji Philippe Coutinho da kuma Arthur.
Man Utd 0-1 Barcelona
Za ku iya auna kwazon 'yan wasan sai ka latsa nan Manchester United da Barcelona
Ajax 1-1 Juventus
Ajax sai kai hare-hare take yi. Wasannan zai fi zafi a zagaye na biyu idan har suka tashi hakan.
Man Utd 0-1 Barcelona
Luke Shaw, wanda aka bai katin gargadi ya taba kwallo da hannu amma alkalin wasa bai kula ba.
Shaw yana cikin masu tsaron baya uku na United a karawar da take son farke kwallo.
Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook