Ronaldo ya ci kwallo 125 a Champions League

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 125 a wasa 161 da ya yi a gasar Champions League.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba nine Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke yi muku sai da safe.

  2. Za su buga wasa na biyu na daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai ta Champions League tsakanin Manchester United da Barcelona da fafatawa tsakanin Ajax da Juventus ranar 16 ga watan Afirilu.

  3. Man Utd 0-1 Barcelona

    Za ku iya auna kokarin 'yan wasan kan rawar da kowanne ya taka latsa nan Manchester United da Barcelona za ku iya yin hakan kafin minti 30 bayan da aka tashi wasa

    Gasa

    Asalin hoton, BBC Sport

  4. An tashi wasa Man Utd 0-1 Barcelona

  5. An tashi wasa Ajax 1-1 Juventus

  6. Man Utd 0-1 Barcelona

    Har yanzu dai Manchester United ba ta buga kwallo ta nufi raga ba

    Kawo yanzu dole United ta ci kwallo idan ta je Nou Camp a wasa na biyu ranar 16 ga watan Afirilu.

    Gasa

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Ajax 1-1 Juventus

    Dan wasan Juventus wanda ya shiga fili daga baya Douglas Costa ya wuce dan wasa daya ya buga kwallo sai dai ta bugi turke.

    Gasa

    Asalin hoton, Reuters

  8. Man Utd 0-1 Barcelona

    Lionel Messi ya yi bugun tazara kwallo ta bugi kafafuwan katangar United, kuma cikin ruwan sanyi David de Gea ya kama kwallo.

    Gasa

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Man Utd 0-1 Barcelona

    Sergi Roberto na tabuka wa tun shigarsa karawar yana ta wataya wa kamar yadda yaga dama, Barcelona ta samu bugun tazara irin wajen da Messi ke cin kwallo.

  10. Ajax 1-1 Juventus

    Ajax ba ta sa'a a karawar nan, wanda ya shiga fili daga baya Jurgen Ekkelenkamp ya kai hari mai kyau raga, amma kuma Wojciech Szczesny ya hana ta shiga raga.

  11. Man Utd 0-1 Barcelona

    Lionel Messi ya karbi kwallo sai dai McTominay ya tokare shi domin hana dan wasan motsa wa ya kuma amfana da hakan.

    Gasa

    Asalin hoton, Reuters

  12. Man Utd 0-1 Barcelona

    Jesse Lingard ya karbi katin gargadi lokacin da ya taba Arturo Vidal, kuma a kusa da Luca Rocchi.

  13. Man Utd 0-1 Barcelona

    Diogo Dalot, wanda yake buga wasa ta gefe mafi lokaci ya fita, an kuma maye gurbinsa da Jesse LIngard.

  14. Man Utd 0-1 Barcelona

    Har yanzu babu wani kwallo da Manchester United ta buga ta nufi raga.

  15. Man Utd 0-1 Barcelona

    Romelu Lukaku ya fita, inda Anthony Martial ya canje shi, kuma an yi masa tafi a filin yadda ya kamata.

    Sai dai Lukaku shi ne wanda yake da karancin taba kwallo a karawar.

    Gasa

    Asalin hoton, Reuters

  16. Man Utd 0-1 Barcelona

    Dan wasan Barcelona Sergi Roberto da kuma Arturo Vidal sun shiga fili, inda aka canmji Philippe Coutinho da kuma Arthur.

    Gasa

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Ajax 1-1 Juventus

    Ajax sai kai hare-hare take yi. Wasannan zai fi zafi a zagaye na biyu idan har suka tashi hakan.

  18. Man Utd 0-1 Barcelona

    Luke Shaw, wanda aka bai katin gargadi ya taba kwallo da hannu amma alkalin wasa bai kula ba.

    Shaw yana cikin masu tsaron baya uku na United a karawar da take son farke kwallo.

  19. Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook