Ministar Ƙwadago a Najeriya, Nkeiruka Onyejeocha, ta nemi gamayyar kungiyar 'yan ƙwadago da na 'yan kasuwa su nuna kishin kasa wajen gabatar da bukatunsu a tattaunawar da ake cigaba da yi kan mafi karancin albashi.
Onyejeocha ta bayyana haka cikin wata sanarwa da daraktan kula da bayanai da hulda da mutane Mista Olajide Oshundun ya saka wa hannu.
A cewar rahoton NAN yayin taron tattaunawa kan karancin albashi da aka yi a ranar Talata, gwamnatin tarayya ta gabatar da naira 60,000 a matsayin sabon albashi mafi karanci ga ma'aikata.
Yayin da kungiyoyin kwadago suma suka gabatar da naira 494,000 a matsayin nasu sabon albashi mafi karanci na ma'aikata da suka tsayar.
Ministar ta kara da cewa gwamnatin tarayya na cigaba da bin matakai domin tabbatar da yin samar da albashi mafi dacewa ga ma'aikatan Najeriya.
Ta kuma cewa, "gwamnati na cigaba da jajircewa wajen fifita al'amuran yan kasarmu kuma tana bukatar duk wandanda abun ya shafa da suyi nuni da fahimtuwa da son kasa".
A cewar ministan, "bayan la'akari da yanayin tattalin arziki da ake ciki yanzu, mun yanke hukuncin kara albashin daga naira 57,000 zuwa 60,000".
A karshe tayi nuni da yadda karin albashin ya zama wata alama da ke nuni da niyyar gwamnati wajen sauraren korafe-karafen kungiyoyin gwadagon domin cimma da yarjejeniya tsakaninta da su.