'Yan Afirka ta Kudu sun fara jefa ƙuri'a a babban zaɓe
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 29 ga watan Mayun, 2024.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail, Haruna Kakangi and A'isha Babangida
Rufewa
To jama'a masu bibiyar wannan shafi namu na BBC Hausa da ke kawo muku labarai kai tsaye, a nan za mu dakata a yau Laraba.
Sai kuma gobe da safe, Alhamis, 30 ga watan nan na Mayu, 2024, idan Allah Ya kai mu za mu sake dawowa.
Kafin sannan a madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad, nake mana fatan alheri, mu kwana lafiya.
Ga wani karin magana mu rufe da shi - Sarki goma zamani goma
Brazil ta janye jakadanta daga Isra'ila kan ɓacin ranta da yaƙin Gaza
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Brazil ta jima tana taƙun saƙa da Isra'ila kan rikicin na Gaza
Brazil ta janye jakadanta daga Isra'ila bayan watanni da suka kwashe suna tankiya tsakaninsu kan rikicin Gaza.
Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya sha sukar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa da sunan ramuwa kan Hamas da kuma irin kisan da take yi wa Falasdinawa.
Mista Lula ya sha kwatanta hare-haren da Isra'ila take kai wa da kisan kiyashin da Nazi suka yi wa Yahudawa.
Zuwa lokacin rubuta wannan labarai Isra'ila ba ta ce komai ba kan wannan batu.
Gwamnatin Masar za ta ƙara farashin burodi
Firaiministan Masar ya sanar da cewa farashin burodi a kasar zai ninka sau hudu daga farkon watan Yuni. Mostafa Maɗbuly ya ce farashin zai tashi ya karu da kashi 40, daidai da rabin santin kudin Amurka.
Wannan ne karon farko da aka samu irin wannan tashin farashin a kasar cikin gwamman shekaru.
Lamarin zai shafi sama da Misirawa miliyan 60 da ke amfana da tallafin burodi da gwamnatin kasar ke bayarwa.
Ƴanbindiga sun kashe mutum 12 da jikkata 20 a kasuwa a jihar Kaduna
Asalin hoton, OTHERS
Ƴanbindiga sun kai hari inda suka kashe mutum 12 a kasuwar Maro, wadda ke ci mako-mako, a ƙaramar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Wani tsohon shugaban ƙaramar hukumar, Cafra Caino,wanda ya tabbatar wa da jaridar Punch labarin kamar yadda ta ruwaito, ya ce ƴanbindigar sun yi wa kasuwar dirar-mikiya ne ana tsaka da hada-hada yau Laraba da misalin ƙarfe 3 na rana, inda suka buɗe wuta.
Ya ce an samu gawarwakin mutum 12, yayin da aka garzaya da wasu mutun 20 da suka ji raunuka asibiti.
Mista Cafra, wanda ya ce wannan shi ne karo na biyu a baya-bayan nan da aka kai wa kasuwar hari ana tsaka da hada-hada, ya ce lokacin daka kai harin jami'an tsaro da ke yankin sun riga sun tafi.
Jaridar ta ce, kakakin rundunar ƴansandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan bai amsa kiran da saƙon da suka aika masa ba, kan lamarin.
Umar Big Show: Matashin da ke gyara wankan taurarin Kannywood
'Najeriya ta tashi tsaye don hana mayar da ɗaliban ƙasar gida daga Birtaniya'
Gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye domin ganin ta hana mayar da ɗaliban ƙasar da ke karatu a jami'ar Teesside, da ke Birtaniya, gida.
Wata tawaga ƙarƙashin jagorancin wakilin ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya, Ambassada Christian Okeke, tare da shugabannin ƙungiyar ɗaliban Najeriyar a Birtaniya, za su gana domin samun mafita.
An ɗauki wannan mataki ne bayan wata ganawa da aka yi ta intanet, wadda shugabar hukumar da ke kula da ƴan Najeriya da ke waje, Abike Dabiri-Erewa, ta yi da Amabasada Okeke, da shugaban ƙungiyar ɗaliban Najeriya a Birtaniya, Yemi Soile, da ɗaliban da abin ya shafa da dama.
A ranar Lahadi ne aka yi taron.
A yau Laraba ne kakakin hukumar (NiDCOM), Abdur-Rahman Balogun, ya tabbatar da matakin sasantawar a wata sanarwa da ya fitar.
Lamarin ya ɗauki hankali ne bayan da wasu daga cikin ɗaliban jami'ar suka yi zanga-zanga ranar 22 ga watan nan na Mayu, 2024, kan umarnin da jami'ar ta bai wa ɗaliban su bar Birtaniya saboda rashin biyan kuɗin makaranta.
Najeriya ta sauya taken ƙasa
Gobara ta laƙume dukiya ta miliyoyin naira a wata kasuwa a Lagos
Aƙalla shaguna 300 ne da aka gina da katako suka ƙone a wata gobara da ta tashi yau Laraba, a kasuwar Tejuosho, da ke Legas, sakamakon tukunyar gas da ake zargin ta fashe.
Gobarar wadda ta ɓarnata dukiyar da ta kai da miliyoyin naira, ta tilasta wa jama'ar da ke zaune a yankin tserewa, da ta tashi bayan ƙara mai ƙarfin gaske da aka ji.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta ce an yi nasarar shawo kan gobarar, kuma an ci gaba da aikin ceto.
Sai dai kuma bayanai sun ce ba a san takamaimai abin da ya haddasa gobarar ba, yayin da wasu ke cewa tukunyar gas ce ta face, wasu kuma na cewa a wajen sayar da gas ne fashewar ta faru.
Binciken farko-farko ya nuna ba mutumin da ya rasu ko kuma ya ji rauni.
Ɗaliban Ghana da ke karatu a waje na tsaka-mai-wuya saboda rashin kuɗi
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ɗaliban Ghana ta nuna damuwa sosai a kan halin da ɗaliban ƙasar da ke karatu a ƙarƙashin tallafin karatu na gwamnatin ƙasar a waje suke ciki.
Rahotanni na cewa yawancin ɗaliban ba su samu kuɗaden da gwamnati ke biyansu ba tsawon wata da watanni, lamarin da ya jefa su cikin wani mawuyacin hali.
A wata sanarwa da ƙungiyar ɗaliban ta fitar yau Laraba ta bayyana cewa hatta abinci da audugar mata na neman gagarar da dama daga cikin ɗaliban.
Shugaban ƙungiyar ɗaliban ta Ghana, Kyeremeh Oppong Daniel, a sanarwar, ya koka da cewa, ɗaliban Ghana da ke karatu a Moroko da waɗanda suke Birtaniya da waɗanda suke Indiya da kuma yawancin waɗanda suke karatu a ƙarƙashin tsarin bashin karatu na gwamnati suna cikin wahala sosai.
A ranar Litinin ɗaliban Ghana da ke Moroko suka gudanar da zanga-zanga a ofishin jakadancin ƙasarsu inda suke neman a ba su kuɗaɗensu, da ba a biya su ba tsawon wata 10 inda wasunsu ke fuskantar kora daga gidajen da suke.
Bayern Munich ta kammala daukar Kompany sabon kociyanta
Sojojin Nijar sun kama Ɓaleri, ɗanbindigar da Najeriya ke nema
Jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun yi nasarar cafke ƙasurgumin ɗanbindigar nan Ɓaleri, wanda ake nema ruwa a jallo a Najeriya.Dakarun runduna ta musamman da ake yi wa laƙabi da Farautar Bushiya (Faraoutar Bushiya), sun kama shi ne a garin Rigar Kowa Gwani, da ke yankin Gidan Rumji a jihar Maraɗi.
A sanarwar da hukumomin sojin Nijar suka bayar, sun ce an damƙe Ɓaleri ne da misalin ƙarfe 1 na rana a lokacin ya yake wata ganawa da yaransa kan yadda za su kai hari Najeriya da Nijar.
Rahotanni sun ce Ɓaleri wanda ɗan asalin Shinkafi ne a jihar Zamfara, wanda ya tsere daga Najeriya , ya jima yana addabar jama'a a yankunan jihar ta Zamfara da kuma Maraɗi a Nijar.
Kuma makusanci ne ga ƙasurgumin ɗanbindigar nan da shi ma ya yi ƙaurin suna a arewacin Najeriya, Bello Turji.
Ɓaleri shi ne na 40 a jerin mutanen da hukumomin sojin Najeriya suka fi nema ruwa a jallo, inda aka sanya lada na musamman ga duk wanda ya kama shi ko ya bayar da labarin inda za a same shi.
Gwamnatin jihar Enugu ta hana bin umarnin ƙungiyar IPOB gobe Alhamis
Asalin hoton, Peter Ndubuisi Mbah/X
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Enugu, Peter Ndubuisi Mbah
Gwamnatin Jihar Enugu ta gargaɗi ƴan haramtacciyar ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) a kan yin ƙafar-ungulu ga jarrabawar kammala babbar sakandire (SSCE) da za a yi a gobe Alhamis.
A yau Laraba ne gwamnatin jihar ta fitar da gargaɗin bayan da haramtacciyar ƙungiyar ta IPOB, ta buƙaci jama'a da kada su fita, su zauna a gida, a gobe Alhamis 30 ga watan Mayu, 2024, domin tunawa da ƴan Biafra da suka mutu a lokacin yaƙin basasa na Najeriya.
A gobe Alhamis za a yi jarrabawar lissafi ne ta kammala babbar sakandire ta SSCE (Theory and Objectives)
A sanarwar da kwamishinan yada labarai na gwamnatin jihar ta Enugu ya fitar ya ce umarnin ƙungiyar ya saɓa da magabatansu suka yi yaƙi a kai.
Gwamnatin ta buƙaci ɗalibai da duk wadanda suke da hannu a jarrabawar da sauran masu harkokin kasuwanci da su fito su ci gaba da gudanar da harkokinsu, da cewa ta tanadi matakan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.
Umar Big Show: Matashin da ke gyara wankan taurarin Kannywood
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Umar Muhammed wanda aka fi sani da Big Show ƙwararre ne a harkar wanka, shi ya sama ya zama mai zaɓa wa shahararrun taurarin masana'antar Kannywood kayan sawa.
Duk da cewa shi ma mawaƙi ne, amma ya ce cikin taurarin da yake zaɓar wa kayan sawa akwai irin su Adam A. Zango da kuma mawaƙa kamar Hamisu Breaker da Umar M Sharif.
'Ya kamata ƙungiyoyin NLC da TUC su tausasa kan albashi mafi ƙanƙanta'
Asalin hoton, Nkeiruka X
Ministar Ƙwadago a Najeriya, Nkeiruka Onyejeocha, ta nemi gamayyar kungiyar 'yan ƙwadago da na 'yan kasuwa su nuna kishin kasa wajen gabatar da bukatunsu a tattaunawar da ake cigaba da yi kan mafi karancin albashi.
Onyejeocha ta bayyana haka cikin wata sanarwa da daraktan kula da bayanai da hulda da mutane Mista Olajide Oshundun ya saka wa hannu.
A cewar rahoton NAN yayin taron tattaunawa kan karancin albashi da aka yi a ranar Talata, gwamnatin tarayya ta gabatar da naira 60,000 a matsayin sabon albashi mafi karanci ga ma'aikata.
Yayin da kungiyoyin kwadago suma suka gabatar da naira 494,000 a matsayin nasu sabon albashi mafi karanci na ma'aikata da suka tsayar.
Ministar ta kara da cewa gwamnatin tarayya na cigaba da bin matakai domin tabbatar da yin samar da albashi mafi dacewa ga ma'aikatan Najeriya.
Ta kuma cewa, "gwamnati na cigaba da jajircewa wajen fifita al'amuran yan kasarmu kuma tana bukatar duk wandanda abun ya shafa da suyi nuni da fahimtuwa da son kasa".
A cewar ministan, "bayan la'akari da yanayin tattalin arziki da ake ciki yanzu, mun yanke hukuncin kara albashin daga naira 57,000 zuwa 60,000".
A karshe tayi nuni da yadda karin albashin ya zama wata alama da ke nuni da niyyar gwamnati wajen sauraren korafe-karafen kungiyoyin gwadagon domin cimma da yarjejeniya tsakaninta da su.
Kamaru ta maye gurbin koci Brys bayan cacar baki da Eto'o
Burinmu shi ne a bar yara su je makaranta a Kebbi - Zainab Nasir Idris
Ƴan bindiga na samun bayanai fiye da yadda muke samu - Dikko Radda
Asalin hoton, fb/Dikko Umaru Radda
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ce suna fuskantar matsala a yakin da suke da yanbindiga saboda "suna samun bayanai fiye da yadda muke samu".
Gwamnan ya faɗi hakan ne a wani taron manema labaru da ya gabatar a Katsina, babban birnin jihar.
Katsina na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fuskantar matsalar ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
Kuma ana ganin cewa matsalar tana ƙamari sanadiyyar mutanen da ke kwarmata wa ƴan bindigar bayanan al'umma.
Dikko ya ce: "Makahon yaki ne ake yi da yan bindiga saboda ba ka sanin waye makiyinka ko masoyinka saboda wani lokaci duk da masu ba su bayanai muke tare saboda haka kowa sai ya zama ɗan sandan kan shi wajen samar da tsaro.
“Muna tattaunawa kan matsalar tsaro amman muna gamawa za su samu dukkan bayanan da aka tattauna”.
Gwamna Radda ya ce har yanzu yana kan bakansa na cewa kowane bangare yana da hannu cikin rashin tsaro a Najeriya.
“Mun kama sarakai da jami’an gwamnati da ke da hannu cikin matsalar tsaro a jihar Katsina, mun kuma samu bayanai da dama dake tabbatar da hakan”.
Tinubu ya saka wa dokar sabon taken Najeriya hannu
Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya saka hannu kan dokar da ta dawo da amfani da tsohon taken ƙasar mai suna "Nigeria: We Hail The".
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar a yau, wanda tuni aka yi amfani da shi lokacin da Tinubu ya yi wa taron majalisar na haɗin gwiwa jawabi a yau Laraba.
Shi ne karon farko da majalisar ta rera taken tun bayan daina amfani da shi shekara 46 da suka wuce.
Shugaba Tinubu ya ce taken na nuna bambancin al'adu, da kuma wakiltar kowane ɓangare tare da zimmar taka rawa wajen ƙulla 'yan'uwantaka.
Yayin bikin cikarsa shekara ɗaya a kan mulki da kuma murnar cika shekara 25 da komawa mulkin dimokuraɗiyya, shugaban ya taya 'yan ƙasa murna kuma ya nemi 'yan majalisa "su ci gaba da aiki tare don gina ƙasar da na gaba za su yi alfahari da ita".
Burinmu shi ne a bar yara su je makaranta a Kebbi - Zainab Nasir Idris
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Za mu tabbatar da umarnin gwamnati kan hana zanga-zanga a Kano - 'Yansanda
Asalin hoton, NG Police
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta ce za ta aiwatar da dokar gwamnatin jihar da ta haramta duk wani nau’in taro da zimmar gudanar zanga-zanga a faɗin jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da jani-in-jaka tsakanin Sarki Muhammadu Sanusi na biyu da kuma Sarki Aminu Ado Bayero.
Kowane bangare ya kafe kan ikirarin da yake na samun umarnin kotu da ya ba shi damar cigaba da jan ragama a inda yake.
Latsa hoton ƙasa ku ji rahoton Zahraddeen Lawan:
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku ji rahoton Zahraddeen Lawan: