A yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihohin Kogi da Imo da Bayelsa, bari mu yi duba kan zaɓen na yau.
An samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri'a a zaɓukan jihohin uku.
Sannan kuma an samu rahotonnin zarge-zargen cike takardun sakamakon tun kafin fara kaɗa ƙuri'a a wasu yankunan jihohin uku.
A jihar Kogi da ke arewa ta tsakiyar Najeriya hukumar INEC ta soke zaɓe a wasu mazaɓun jihar, sakamakon zargin cike takardun sakamako, tun kafin fara kaɗa ƙuri'a.
A jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin ƙasar, an samu rahotonnin garkuwa da jami'in zaɓe, kodayake daga baya INEC ɗin ta ce an sako shi
Mai sanya idanu na cikin gida a zaɓen ya shaida wa manema labarai cewa an samu rahotonnin razanar da masu kaɗa ƙuri'a da rigingimu a jihar ta Bayelsa.
A jihar Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar kuwa, an ga wasu mazauna jihar na kan layin ɗiban ruwa a maimakon layin zaɓe.
Sun ce babu wutar lantarki da ruwan sha a jihar, sakamakon yajin aikin ƙungiyar kwadago a jihar.
Gwamnan jihar Hope Uzodinma na neman wa'adin mulki na biyu a zaɓen.